Hikimar Ziyarar Kaburbura



 Saboda haka kiran da a aka yi a cikin dukkan wadannan hadisai guda biyu da cewa "ku ziyarci kaburburaâ€‌ duk da cewa ya fuskantar maza ne amma sakamakon haka ya hada maza da mata ne.

 Bayan wannan hadisi kuma a kawai wasu ruwayoyi da suke nuni da halascin ziyarar kabari ga mace, saboda haka a nan zamu ambaci wadannann hadisai kamar haka:

1-Muslim yana ruwatowa a cikin sahih dinsa daga manzo cewa: Jibril ya sauko zuwa gare ni ya ce da ni: Ubangijinka yana ba da umarni da a ziyarci kaburburan mutanen “Bakiyyaâ€‌ Sannan ka nema musu gafara a wajen Allahâ€‌.

 Sai manzo ya tashi daga bisa shimfidarsa ya tafi Bakiyya domin ziyara, sai A’isha ta bi manzo (S.A.W) daga baya, sai ta fahimci umarnin da Allah ya aiko wa manzo.

A lokacin sai ta tambayi manzo cewa: to yaya zan ziyarci mutanen baki? Sai manzo ya ce: “Ki ce amincin Allah ya tabbata ga nutanen wannan gida daga musulmai da muminai, Allah ya gafarta wa wadanda suka riga mu da wadanda zasu zo bayammu. [14]

Wurin da ake kafa dalili a nan shi ne wajen koyar da A’isha yadda ake ziyara, saboda haka idan ya zamana bai halitta ba mace ta ziyarci makabarta, a nan babu ma’ana manzo ya koyar da matarsa.

 Sannan bugu da kari A’isha ta kasance tana gaya wa sauran mata dangane da abin da ya auku, saboda haka da wannan zamu iya gane cewa ya hada kowa da kowa cewa ziyarar baki daya ta halatta ga mace da namiji. Domin kuwa matar manzo da sauran mata duk daya suke a wajen hukuncin Allah!

2-Fadima (A.S) â€کyar manzo (S.A.W), kuma daya daga cikin mutanen mayafi (wadanda aka saukar da aya ta 33 suratul ahzab a kansu) Bayan wafatin manzo ta kasance tana ziyartar kabarin amminta wato shahidin Uhud inda take yin salla raka’a biyu sannan ta yi kuka a kabarinsa.

 Hakim Nishaburi bayan ya ruwaito wannan ruwaya yana cewa: wadanda suka ruwaito wannan ruwaya dukkansu amintattu ne kuma adalai, ta wannan fuskar ba su da bambanci da maruwaitan Bukahri da Muslim[15].

 3-Tirmizi ya ruwaito daga Abdullahi Bn Abi Malika yana cewa: Lokacin da Abdurrahman bn Abibakar ya rasu a wani wuri da ake kira da (Hubsha) Sai aka dauki jana’izarsa zuwa Makka aka rufe shi a can. Bayan wani lokaci sai A'isha wadda take â€کyar uwa ce a gare shi ta zo Makka domin ziyarar kabarin Abdurrahaman dan’uwanta, Sannan ta yi wasu wakoki guda biyu wadanda suke nuna tsananin damuwarta a kan rashinsa.[16]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next