Hikimar Ziyarar Kaburbura



 Ã¢â‚¬Å“Amincin Allah ya tabbata gareku ya gidan mutane muminai kun samu abin da ake alkwari da zuwansa a gaba, Kuna rayuwa tsakanin mutuwa da tashin kiyama, mu ma zamu hadu daku, Ya Allah ka gafarta wa wadanda suke a cikinâ€‌ Bakiyyaâ€‌.

2-Muslim a cikin Sahih dinsa ya ruwaito daga A’isha tana cewa Manzo ya ce mata: Jibril ya sauka zuwa gareshi ya ce masa Allah yana ba da umarni da cewa ku tafi ziyarar mutanen “Bakiyyaâ€‌ Sannan ku nema musu gafara.

 A’isha tana cewa: Sai na tambayi manzo cewa, yaya za yi musu addu’a? Sai manzo ya ce ki ce: “Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku mutanen wannan gida daga muminai da musulmai, Allah ya jikan wadanda suka riga mu da wadanda zasu zo bayanmu daga cikinsu, Mu ma insha Allah muna nan zuwa mu hadu da kuâ€‌. [11]

3- Muslim yana ruwaitowa daga Buraida cewa: Manzo (S.A.W). ya kasance yana koyar da Sahabbansa cewa yayin ziyara ga abin da zasu ce: “Amincin Allah ya tabbata a gare ku ya ku mutanen wannan gida muminai muna nan zamu hadu da ku, Muna rokon Allah da ya ba mu lafiya tare da ku.[12]

Mata Da Ziyarar Kabari

 Mata suna da hukunci guda ne da maza dangane da ziyarar masoyansu da waliyyan Allah, domin kuwa hukuncin maza da mata a cikin musulunci duka abu guda ne, sai kawai wurin da aka bambanta maza da mata a wasu wurare na musamman tare da dalili.

 Manzo (S.A.W) Yana kira zuwa ga musulmi da cewa: “Ku ziyarci kaburbura domin suna tuna muku lahiraâ€‌.

 Sanan a wani hadisi daban yana cewa: “Ku ziyarci makabarta domin akwai darasi a cikin yin hakanâ€‌.

 Gaskiya ne wadannan kira tare da lura da yadda aka amfani lamirin maza kamar ya nuna cewa da maza ake, amma kamar yadda muka tunatar cewa kusan dukkan kira da ake yi a cikin Kur’ani da hadisi kamar ana kira ne zuwa ga maza, saboda haka dukkan ayoyin da aka yi amfani da su wajen umartar mutane a kan yin salla da azumi da wannan sigar ne wato an yi amfani da lamirin maza ne, amma wannan umarni ya kunshi mata kamar yadda ya kunshi maza. Kamar yadda yake cewa: Ku tsayar da salla ku bayar da zakka duk abin da kuka gabatar domin kawunanku na alheri to zaku same shi a wajen Allahâ€‌[13].

 Wannan umarni bisa lura ga ka’idar larabci kamar yana fuskantar maza ne, amma wannan hukunci ya kunshi duka maza da mata ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next