Hikimar Ziyarar Kaburbura



1-Tunawa da musulman farko wadanda suka kasance cikin mawuyacin halin yakin Khandak amma a cikin wannan hali ne suka gina wadannan masallatai don su yi salla kuma suka cigaba da yakinsu. Domin kuwa wasu daga cikin wadannan masallatai suna wuraren da aka gwabza tsakanin sojojin tauhidi da na shirka yayin da aka kashe gwarzon shirka (Amru bn Abdu wud) kuma sakmakon haka ne gwamnatin dagutu ta kawo karshe.

Halartar musulmi a wadannan wurare tana tuna musu da wadannan abubuwa da suka faru a wannan wuri, sannan yana kara karfafa alakarsu da wadancan musulman farko.

2-Amma ma’ana ta biyu kuwa da zata iya zama dalilin da ya sa musulmai suke zuwa wadannan masallatai ita ce, domin neman tabarraki daga wadannan wurare, domin jinanan shahidai a kan hanyar tauhidi a wadannan wurare ne ya zube, Saboda haka wannan wurare sun sheda kai da kawon shahidan musulunci, sannan kuma wuri na kai-da-kawon manyan musulmai.

Wadannan manufofi su ne suke sanya musulmi suna tafiya zuwa wadannan wurare da makamantansu, kamar wurin da aka yi yakin khaibar da Fadak, duk sun samo asali ne daga wadannan manufofi guda biyu.

Amma yin salla a wadannan wurare bayan musulmi sun shiga wadannan masallatai domin aiwatar da umarnin ubangiji cewa duk yayin da mutum ya shiga wani masallaci to ya gabatar da salla raka’a biyu a matsayin gaisuwa ga shi masallacin. Saboda haka ba wannan ba ne hadafinsu na zuwa wadannan masallatai ba domin su gabatar da salla a wajen. Wannan niyya tana zuwa ne bayan sun shiga masallatan.

Girmama Kaburbura Masu Tsarki

Al’ummun da suke raye a kasashen da suka cigaba a duniya zaka ga suna kokari wajen kare kayan tarihi kuma suna nuna soyayyarsu ga wadannan abubuwa na tarihi. Sannan suna iya kokarinsu da su kare wadannan kayan tarihi don kada su bata ko su lalace. Domin kiyaye wadannan kayan tarihi kuwa wadanda suke nuna cigabn su a tsawon tarihi har ma’aikatu na musamman suka samar da ma’aikata kwararru domin kawai wannan aiki. Sakamakon haka ne ba su ba da wata dama da zata sanya wani guntun abu daga cikin wadannan kayan tarihi da suka hada da wani allo wanda aka yi wani rubutu a kai ko guntun jirgin ruwa da ya bata. Domin sun yi imani da cewa wadannan kayan tarihi suna ba da wata sheda ce ta musamman ta su wadannan al’umma. Mutanen da suka yanke daga al’ummarsu da manyan tarihinsu da suka gabata suna da hukuncin yaro ne wanda ya bata daga hannun iyayensa.

 Cigaban musulunci wani cigaba ne wanda yake mai girman gaske wanda a karnonin tsakiya shi ne kawai cigaban da babu kamarsa.

Sakamakon koyarwar da Musulmai suka samu daga littafinsu na sama, sun kafa cigaban da ba a taba yinsa ba a tarihi. Wanda ya kai kololuwarsa a cikin karni na hudu, ta yadda gabas da yammacin duniya suka shaida haka, kamar yadda ya gina Tajmahal na kasar Indiya da Kasar (Spain) sauran gine-gine masu ban al’ajabi, wanda ta hanyar kaitsaye ko kuma ba kaitsaye ba. Kamar yadda masana na yamacin duniya suka tabbatar da cewa cigaban yammacin duniya ya samu asali ne ta hanyar Andulus ko kuma ta hanyar yakin da ya auku tsakanin musulmi da kiristocin yammacin duniya.

 Cigaban musulunci ya fara ne da aiko manzon Musulunci (S.A.W) ko kuma da wata ma’ana ya fara ne da haihuwar shi manzon, Sannan da taimakon mabiyansa ya cigaba ta kafuwa da yaduwa a sauran sassan duniya. Gine-ginen da suke dangane da Manzo ko kuwa wasu daga cikin sahabbansa suna daga cikin wannan cigaba na musulunci. Sannan kuma wannan ba mallakin wani ba ne ta yadda zai yi abin da ya ga dama da su, wannan na dukkan al’ummar musulmi ne. Saboda haka babu wata hukuma ko wasu mutane da zasu yi abin da suka dama da wannan kayan tarihi da cigaban musulunci ba tare da izinin sauran musulmi ba. Ta yadda ta hanyar yaki da bidi’a da tsayar da tauhidi su kawar da wadannan kayan tarihi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next