Hadisan Annabi



Ka kyautata wa wanda ya munana maka.


قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: المُسلِمُ مَن سَلِمَ المُسلِمونَ مِن لِسانِهِ ويَدِهِ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce :

Musulmi shi ne wanda musulmi suka kubuta daga harshensa da hannunsa.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنّي أمزَحُ ولا أقولُ إلّا حَقاً .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce :

Ni ina yin raha amma ba na fada sai gaskiya.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله:النَّظَرُ سَهمٌ مَسمومٌ مِن سِهامِ إبليسَ فَمَن تَرَكَها خَوفاً مِنَ اللهِ أعطاهُ إيماناً يَجِدُ حَلاوَتَهُ في قَلبِهِ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce :

Kallo (zuwa ga haram) kibiya ce daga kibiyoyin Iblis duk wanda ya bar shi saboda jin tsoron Allah, zai ba shi imanin da zai ji dadinsa a zuciyarsa. 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next