Hadisan Annabi



قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: لَو اُتِيتُ بِشابٍّ مِن شَبابِ الشِّيعَةِ لا يَتَفَقَّهَ (في الدِّينِ) لَأَدَّيتُهُ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce :

Da za a zo mun da wani saurayi daga samarin shi’a da baya neman ilimin addini da na ladabatar da shi.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: فَضلُ الشّابِّ العابِدِ الَّذي تَعَبَّدَفي صِباهُ عَلَى الشَّيخِ الَّذي تَعَبَّدَبَعدَ ما كَبُرَت سِنُّهُ كَفَضلِ المُرسَلينَ عَلى سائِرِ النّاسِ.

Manzon Allah (S.A.W) ya ce :

Fifikon saurayi mai ibada wanda yake bauta a kuruciyarsa akan tsohon da yake bauta bayan ya manyanta kamar  fifikon manzanni ne akan sauran mutane.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنَّ اللهَ يُحِبُّ الشّابَّ الَّذي يُفنيشَبابَهُ في طاعَةِ اللهِ عزّوجلّ

Manzon Allah (S.A.W) ya ce :

Allah yana son bawan da yake karar da samartakarsa wajan bin (bautar) Allah (SWT) .

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله:إنَّ الله تَعالى يُباهي بِالشّابّ ِالعابِدِ المَلائِكةَ ، يَقولُ : اُنظُرُواإلى عَبدي! تَرَكَ شَهوَتَهُ مِن أجلي .



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next