Hijabi Lullubin Musulunci



" Hakika mace Ba'italiya tana tsoron fita daga gidanta, don kare mutuncinta daga lalatattun samari wadanda suke yawo a kan tituna da kuma wadanda ba su da wani aiki face kai hari ga mataye da budurwaye da kuma sace su da nufin yin fashi ko kuma aikata fyade… hakika mace takan ki yarda da duk wani aiki kome daukakarsa, idan dai har aikin zai kai ta ga dawowa gida cikin dare ne, don kada ta sanya mutunci da lafiyarta cikin hatsari"[14]. A wani rahoto da kungiyar Kulawa da Iyali ta kasar Amirka ta buga ta bayyana cewa:

" Lalacewar iyali (aure) wanda ya zamanto ruwan dare, ita ce babbar matsalar da take damun al'umma. Domin a kowace shekara a kan raba auren ma'aurata sama da miliyan daya, wanda haka ya nunka na karnin da ya gabata har sau bakwai."

" Kana yawan shegun 'ya'ya ya karu sau uku in aka yi la'akari da na shekarar 1938, sannan a duk shekara a kasar Amirka a kan haifi shegun 'ya'ya sama da miliyan hudu. Sannan dangane da matsalar lalacewar matasa kuwa wanda hakan yana da alaka da irin rabe-raben aure da ke faruwa, kididdigar ta nuna cewa al'amarin ya nunka na shekarar 1940 har sau uku".

Wani rahoton kuma cewa yake:

"A wani rahoton da Hukumar Binciken Laifuffuka ta Kasar Amirka (F.B.I) ta fitar, ya nuna cewa a cikin irin shari'o'in kisan kai da ke faruwa a tsakanin iyalai, sau da dama mazajen ne ke kashe matayen nasu; kana kuma kashi 15 cikin dari na laifuffukan da suka shafi iyali cutarwar da ke cikinsa tana dawowa ne ga yara kanana ne".

Sannan wata kididdiga da kungiyar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta nuna cewa "kashi 60 cikin dari na matan aure a Amirka da Turai sun sami kansu cikin kunci, damuwa da halin kaka-ni-ka-yi"[15]. A lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Dr. Homer wata baturiyar kasar

Sweden kan ta yi bincike kan matsayin mata a kasashen Larabawa a shekarar 1975 , inda ta sanar cewa: " Hakika macen kasar Sweden ce, take da bukatuwa da ta nemi 'yancinta, domin kuwa su matan kasa-shen larabawa sun riga sun sami nasu 'yancin tuntuni karkashin addinin Musulunci". Ta ci gaba da cewa: " a wannan lokaci macen kasar Sweden ta yi ta kokarin ganin an bayyanar da

wannan shekarar a matsayin "Shekarar Mata ta Duniya" kana kuma a sake bayyanar da wata shekarar a matsayin ta mazaje, don ya samu daman kwato hakkokinsa daga wajen mataye.[16]"

Dr. Homer ta ci gaba da cewa: " Kashi 25 cikin dari na matayen kasar Sweden suna fama da ciwon ruhi da na jiki, sannan ana kashe kashi 40 cikin dari na kudin shigar kasar Sweden ne a wajen magance wadannan cututtuka da wannan 'yanci na jeka-na-yika da matayen kasar Sweden suke gudanarwa ya haifar. Hakika, babbar matsalar macen kasar Sweden ita ce irin wannan yanke kauna wanda ya tura ta zuwa ga gabar wani abu mai hatsarin gaske da ke fuskantar rugujewa(1)". Hakika wannan bakar cuta ta haifar da rugujewar zaman lafiyar iyali a kasar Biritaniya, wanda hakan ya haifar da karuwar adadin zaurawa ko kuma maza da matan da suke zaman daduro. A bisa kididdigar da gwamnatin Birtaniya ta buga a ran 14 ga watan Janairun shekarar 1988, ta nuna cewa yawan haihuwar shegun 'ya'ya ya tashi daga kashi 4 cikin dari a shekara ta 1950 zuwa kashi 21 cikin dari na dukkan haihuwar da aka yi a shekara ta 1986, kana in banda kasar Denmark da take da kashi 43 cikin dari, kasar Birtaniya ce take da adadi mafi yawa a duk kasashen Turai. Kididdigar da aka yi ta nuna cewa kasar Biritaniya ce take da adadin shika mafi yawa a kasashen Turai, kusan ninki biyu na kasashen Faransa da Jamus.

An gano cewa tsakanin shekarar 1979 da kuma shekarar 1985, adadin maza da matan da suke zama da junansu ba tare da aure ba, ya kusan ninkuwa. Kana a shekarar 1985, kashi 15 cikin dari na dukkan matayen da ba su da aure, har ma da wadanda aka sake su, suna aikata daduro.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next