Hijabi Lullubin Musulunci



Wasu kuwa sukan yi amfani da wannan hanyar:- Wato lokacin da nakuda ta kama mace sai ta je ta zauna a bakin wani rami (da aka riga aka tona). Idan har ta ga abin da ta haifa mace ce, sai ta jefa ta cikin ramin, kana ta rufe ta da kasa. Idan kuwa namiji ne, sai ta dauke shi zuwa gida !

" Kana wadanda ba sa so su bisne 'ya'yayen nasu mata, sai su barsu cikin wulakanci har su kai shekarun da za su iya yin kiwo, to sai a sanya musu riguna masu gashi a tura su rairayin sahara don kiwon rakuma ! "Sannan wadanda ba sa so su tura ta kiwo, sai su yi amfani da wasu muggan hanyoyi don wulakanta ta. Misali idan yarinyar ta girma ta isa aure sai ayi mata aure, idan mijin nata ya mutu sai uban (waliyin) nata ya zo ya sanya mata wasu irin tufafi na musamman wadanda ke nuna cewa ba ta da wani 'yancin yin aure ba tare da yardar uban nata ba. Ta haka ne za a tilasta mata yin aure ba tare da sonta ba ! To idan shi uban nata ba ya son ya aure ta, to za ta zauna nan a daure har ta mutu, kana kuma sai ya gaje ta. Idan kuwa har tana son ta fanshi kanta daga irin wannan hali, dole ne sai ta bayar da wasu kudade don ta 'yantar da kanta. Wasu kuwa sukan 'yantar da matan, amma fa da sharadin ba za su taba yinaure ba sai dai da izinin waliyin nasu, ko kuma dole ne ta biya diyya. Wasu kuwa sukan ajiye bazawarai wadanda mazajensu suka mutu har sai wani daga cikin 'ya'yayensu kanana ya girma kafin su aurar masa da ita.

" Dangane da mace marainiya kuwa, sukan ajiye ta ne a wajensu kana su hana ta aure da burin cewa za su aure ta lokacin da matayensu suka mutu, ko kuma su sanya ta ta auri daya daga cikin 'ya'yayensu don saboda su sami dukiyarta....[6]

Su kuwa Girkawa, suna ganin mace a matsayin wata doluwar halitta ce da bata da wani 'yanci guda-nar da duk wani al'amari. Hatta wasu daga cikin falasafofin kasar Girka sun dauki kulle mace a cikin gida, kamar sanya ta cikin kurkuku ne. Wani mashahurin mai hikima na kasar Girka, Yosteen cewa yake: " Muna auren mata ne kawai don su samar mana da halaltattun 'ya'yaye"[7]. "Su kuwa Romawa, suna ganin matayensu a matsayin wani kaya maras kima da namiji ya mallaka. Sukan tafiyar da ita kamar yadda suke so. Sun taba yin wani taro a daya daga cikin majalisosinsu a birnin Roma don su tattauna kan al'amarin mata. Inda daga karshe suka kai ma natijar cewa ita (mace) kawai wata halitta ce da bata da kwakwalwa, kana kuma ba ta da wani rabo a rayuwar lahira. Ita kawai wata juji ce, ba za ta ci nama ba kana ba za ta yi dariya ba ko kuma bakin fadin wani abu ba. Dole ne ta tafiyar da rayuwarta cikin bauta da biyayya.

"Wasu daga cikin 'yan majalisar masanan Romawa sun fitar da wata doka da ta haramta wa mata mallakan fiye da rabin miskali na zinare. Dole ne ta sanya tufafi masu launi daban-daban kana kuma ba za ta yi tafiya a cikin keken dawaki na fiye da mil guda a wajen garin Roma ba sai dai in lokacin wani buki ne na gaba daya[8].

Yayin da tarihin Turai yake magana kan kasar Girka ya nuna cewa a wani lokaci Bagirke guda ya kan ajiye mataye dari a gidansa. Kana tsohon tarihin Iran ya bayyana faruwar wasu al'amurra makamantan wadannan na zamanin Jahiliyyar larabawa da kuma tsofin al'adun Turai. Idan ma dai akwai wani banbanci tsakaninsu to sai dai irin na bayani. A matsayin misali, yana da kyau mu yi dubi ga wadannan abubuwa: "A zamanin da a Iran babu wani mutum da yake kange matayensa daga sauran Mutane[9].

Khosrow Parviz (wani sarkin gidan sasaniyawa) ya mallaki mataye kimanin 3000 a cikin fadansa, amma da haka ba su ishe shi ba. Domin duk lokacin da ya ke so ya kawata fadarsa, to sai ya rubuta wasika zuwa ga gwamnoninsa a inda zai ba su siffofin irin macen da yake so. A nan take za su kawo masa irin wannan mace da ya siffanta[10].

A wasu shekaru da suka gabata a kasashen Turai, mutane suna da kuduri kamar haka: Mace ba wai kawai wata alama ce ta rashin da'a, kana kuma matattarar muggan abubuwa da lalacewa ba ne kawai, face ma dai ita ce asalin duk wani bala'i da ka iya samun dan'Adam. Ita ce ummul aba'isin din duk wani tashin hankali da wahala ga mutanen da suke bayan kasa. Sannan wani daga cikin Paparomo-min farko mai suna Tirroliyan ya yi cikakken bayani kan matsayin Kiristanci dangane da mata. Ya ba da gurbataccen ra'ayin Kiristanci dangane da mace; ita ce hanyar da Shaidan yakan bi wajen shiga ruhin mutum. Ita ce wacce ta ingiza mutum zuwa ga haramtacciyar bishiyar nan (da aka hana Annabi Adamu (A.S) cinta), aka saba wa umurnin Allah, wannan ita ce mace.

Dangane da matsayin mace a shekarun da suka wuce ne, malamin falsafan nan na Biritaniya Herbert Spinser yake fadi a cikin littafinsa na "Describing Sociology" cewa:

Hakika a karni na sha daya a Birtaniya, a kan sayar da mace (ga wanda zai aure ta) kana kuma a dai-dai wannan lokacin kuma sai kotuna, wanda dama su ke karkashin majami'ai ne, suka kafa wata doka wacce ta ba wa shi mijin daman chanzata ko kuma ba da hayar matar tasa ga wani namiji daban na wani kayyadad-den lokaci"[11].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next