Hijabi Lullubin Musulunci



Dangane da hijabi ga mace da kuma dangantakarsa da irin al'ummomin da suke kewaye da ita, hakika akwai manyan mahanga guda biyu kan kalmar hijabi cikin karnonin da suka gabata.

Mahangar Lokacin Jahiliyya Kan Hijabi.

Hakika kafin bayyanar Musulunci tsohuwar jahi-liyya ta samu daman kafa munanan manufofinta cikin tarihi, kana kuma mata sun dandani mummunan yanayi na zaluncin irin wancan lokacin. A wancan lokacin al'amari ya munana ta yadda aka kwace wa mace 'yancinta inda har ya kai ma ana ganinta kawai a matsayin wata haja ce ta saye da sayarwa, karkashin irin wannan mummunan tsari. An kwace mata kimarta na dan'Adamtaka, kana aka juya ta ta zamanto wata halitta kawai da mazaje suke amfani da ita don jin dadi, ko kuma a wani lokaci ma a matsayin baiwa.

Lalle koma dai mene ne za a fadi a matsayin shi ne abin da ya sanya mazaje suka shafe matsayin mata da kuma zaluntarsu a rayuwa a wancan lokaci da ya gabata, shin hakan ya faru ne saboda dalilai na tattalin arziki, sha'awa ko kuma dalili na ruhi ko addini, to al'amarin dai a fili yake, shi ne cewa shi wannan tozartarwa ga mace da kuma kwace mata hakkokinta, wannan kwace mata kimarta na dan'Adamtaka ya kai wani matsayi da mutumin wannan zamani ba zai iya suranta shi ba.

Zaluncin da ya faru ga mata yana yawo ne tsakanin wadannan al'amurori na haramci da wa'id da kuma abin da ke tattare da na mummunan akidu da dabi'u wadanda suke da yawa.

Zaluncin da ya faru ga mata yana yawo ne tsakanin wadannan al'amurori na haramci da wa'id da kuma abin da ke tattare da na mummunan akidu da dabi'u wadanda suke da yawa. Wadansu kuma suna ganin mace a matsayin shaidan ne cikin tufafin dan'Adam, don kawai ta bauta wa namiji, kana ya samu biyan bukatunsa ta hanyarta, kamar yadda mutanen Jahiliyya suke gani. Wasu kuwa suna daukan cewa jikinta na mutum ne, amma ranta na dabba ne. Wannan ra'ayi ya samo asali ne daga kasashen Turai kafin sauye-sauyen da aka samu. To mai karatu, ya rage maka ka sauwara irin babban bala'in da ya faru ga mace, lokacin da ake ganinta a matsayin shaidan ko kuma wata dabba ko kuma wata haja abin sayarwa kamar sauran kayayyaki. To wadannan su ne wadansu daga cikin irin wahal-halun da mace ta fuskanta karkashin irin wadannan munanan akidoji.

Lalle Alkur'ani mai girma ya ambaci wasu daga cikin wahalhalun da suka sami mace a karkashin al'ummar Jahiliyya ta Larabawa wanda kuma Musu-lunci ya yi kakkausar suka gare su:

"Kuma idan aka yi wa dayansu bushara da mace, sai fuskarsa ta wuni baka kirin, alhali yana mai cike da bakin ciki. Yana boyewa daga mutane domin munin abin da aka yi masa bushara da shi. Shin zai rike shi a kan wulakanci, ko zai turbude shi a cikin turbaya? To, abin da suke hukumtawa

ya munana".(Surar Nahali: 16:58-59) "Kuma kada ku kashe 'ya'yayenku domin tsoron talauci. Mu ne ke arzurta su, su da ku. Lalle ne kashe su ya kasance kuskure babba". (Surar Isra'i: 17: 31)

"Kuma idan wanda aka turbude ta da rai aka tambaye ta: saboda wane laifi ne aka kashe ta". (Surar Takawiri: 81: 8-9) Kana kuma an ruwaito Annabin rahama (S.A.W) yana cewa: "Wata rana wani mutum mai suna Qais bin Asim al-Tamimi, ya zo wajen Manzon Allah (s) ya ce: " a lokacin Jahiliyya na kasance na bisne 'ya'yayena mata guda takwas..."[5]. Hakika za'a iya bayyana zamanin Jahiliyya na larabawa kafin zuwan Musulunci kamar haka:

"An kasance ana bisne 'ya'yaye mata cikin mummunan yanayi; a kan bisne jariri da rai ! sukan yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen gudanar da wannan al'ada. Idan aka haifa wa daya daga cikinsu diya mace, to sukan bar ta har na tsawon shekaru shida. Daga nan sai mahai-finta ya yi umrnin da a yi mata ado a shafa mata turare da karyar cewa zai kaita wurin danginta ne ! To amma a dai-dai lokacin an riga an tona mata wani rami cikin rairayin sahara. A lokacin da suka isa sai mahaifin nata ya ce mata ta leka ramin, nan take sai ya tura ta cikinsa, kana ya rufe ta da kasa !



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next