Hijabi Lullubin Musulunci



4- Abin Da Ya Hau Namiji da Mace Kan Hijabi

Bari mu yi dubi cikin muhimman al'amurran da suka shafi dukkan jinsunan biyu, don bambance abubuwan da suka hau kansu dangane da wannan muhimmin al'amari na hijabi. Namiji da mace suna da abubuwan da suka hau kansu, kamar yadda wannan aya ta Alku'ani ta bayyana:

"Ka ce wa muminai maza da su kawar da idanuwansu kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce wa muminai mata su kawar da idanuwansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana kawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu…". (Surar Nur 24: 30-31)

Manyan malumman fikihu sun yi bayanin wannan hukumci kamar haka:

(A)- Dole ne mace ta rufe dukkan jikinta daga idon wanda ba muharraminta ba.

(B)- Haramun ne ga mutum ya dubi jiki da gashin macen da ba muharramansa ba, amma ban da fuska da tafukan hannayenta. Kana kuma haramun ne ga mace ta kalli maza in dai ba mahaifanta ko danta ko kaninta ko kakanta ko dan'uwanta da kuma sauran wadanda suke da dangantaka da ita ba.

(C)- Haramun ne ga mutum ya kalli fuska ko hannayen macen da ba muharramansa ba da nufin jin dadi, haka ita ma macen.

(D)- Ya halalta ga mutum ya kalli jikin macen da yake son ya aura don ya ga irin yanayin jikinta, haka ita ma macen.

(E)- Yana halalta namiji ko mace su kalli jikin muharramansu (amma ban da al'auranta) matukar dai ba da niyyar jin dadi ba ne, amma kallo irin na sha'awa yana haramta ga muharramai da ma wadanda ba muharramai ba.

(F)- Wajibi ne ga mace da ta rufe jikinta da kuma gashinta daga idon mazajen da ba muharramanta ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next