Hijabi Lullubin Musulunci



Kasar Japan: A shekaru ashirin da suka gabata, adadin shika ya ninku kashi biyu. Kafin shekarar 1947, mazaje suna da daman shikan matayensu ko da a kan titi ne. to amma yanzu, kashi 70 cikin dari na shikan, matayen ne suke jawo shi.

Kasar Afirka Ta Kudu: Kungiyar kwato hakkin matayen Afirka ta Kudu tana cewa a rayuwar daya daga cikin biyun matayen Afirka ta Kudu ana musu fyade. Hakan kuwa ya hada har da kananan yara da tsofi.

Kasar Biritaniya: Adadin shika a kasar Biritaniya ya dara na kowace kasa a kasashen Yammacin Turai. Kusan mace guda cikin mataye marasa maza guda bakwai masu shekaru 18 zuwa 49, suna zama da wani namiji ba tare da aure ba.

Wata mujallar birnin London mai suna "The Hospital Today", a bugunta na watan Afrilun shekarar1975, ta buga rahoton shekara-shekara na Ma'aikatar Lafiya da Jin Dadin Al'umma ta kasar Biritaniya, inda take cewa: "…..duk da yawan abubuwan hana daukan ciki da kuma halaccin zubar da ciki, to amma duk da haka an gano cewa kashi 86 cikin dari na yara, mata da ba su da maza ne suke haihuwarsu! A nan gaba akwai babban matsala. A shekarar 1973 an sami wadannan rahotanni kamar haka: an sami rahoto guda na wata yarinya 'yar shekara 11 da ciki; rahotanni guda shida na yara 'yan shekaru 12 masu ciki; rahotanni guda 38 na yara 'yan shekaru13 masu ciki; rahotanni 255 na yara 'yan shekaru 14 masu ciki. Kana kuma a dai-dai wannan shekarar an sami rahoton zubar da ciki har guda 166,000, kashi 50 cikin dari na wannan adadi ya faru ne daga mata marasa aure[17]. Idan muka koma ga gabashin (duniya) kuwa, za mu ga lalacewar al'umma a duniyar kwaminisanci ba boyayyen al'amari ba ne a kan na duniyar 'yan jari hujja.

Mujallar "Interphase" a bugunta na watan Afrilun shekarar 1977 ta ba da rahoton cewa: "Babbar matsalar 'yan Gurguzun kasar Sobiyet ita ce cewa, a yammacin kasar Rasha daya daga cikin aurarraki biyu da suke daurawa yana karewa ne ta hanyar shika. Misali, a birnin Mosko, kusan kashi 49 cikin dari na aurarraki, sukan kare ne ta hanyar shika bayan da aka haifi dan farko. A yankin Mavadanski kawai adadin shika ya kai yawan kashi 72.9 cikin dari. A saboda haka ne ma wani taron kara wa juna ilimi na likitoci da aka yi a Jami'ar Mosko a shekarar 1975, taron ya yi

kira da a nemo wata mafita ga wannan matsala ta yawan hauhawar adadin shika da karancin adadin haihuwa[18]". Ko da yake ya kamata a gane cewa wadannan matsaloli na iyali sun ta'allaka ne

kawai ga garuruwan da ba na musulmai ba ne na Tarayyar Sobiyet. Duk da irin hana gudanar da koyarwa irin ta Musulunci a garuruwan musulmai da suke karkashin kasar Sobiyet daga bangaren 'yan Gurguzu, to amma sai da Musulunci ya ci gaba da tasirinsa a rayuwa da dabi'un musulman wadancan garuruwa, yana mai rage matsalolin iyali da kuma wulakanta mata. Wadannan bala'o'i da makamantansu, su ne abubuwan da wannan mahanga ta Turai kan mu'amaloli tsakanin maza da mata ta haifar. A dalilin haka ne, Musulunci ya dauki matakan ruguza tushen lalacewar al'umma da

kuma kokarin tsayar da wulakanci da ake wa mata da kwace musu hakkokinsu kana da kuma tabbatar da mutunci da girmamawa a cikin rayuwar 'yan 'Adam. Don haka, hijabi yana daga cikin mashahuran abubuwan da Ubangiji Ya yi amfani da su wajen kare mutuncin mace da kuma gina tsarkakakkiyar al'umma.

Za mu iya ganin irin halin da ke wanzuwa a da dama daga cikin kasashen musulmai wadanda suka maye gurbin koyarwar Musulunci da na kasashen Turai. Al'ummar wadannan kasashe sun kaurace wa ka'idojin Musulunci, wadanda suka hada har da hijabi, inda suka dauki halayen kasashen Turai a matsayin abin koyi. Don haka ne shika, karuwanci, shaye-shayen giya da muggan kwayoyi, kana da kuma bullar cututtuka irin su ciwon kanjamau (AIDS) da dai sauransu, suka buwayi wadannan al'ummomi da suka zabi su bijire wa ka'idojin addininsu. Kana kuma suka halalta haramtacciyar mu'amaloli tsakanin samari da 'yan mata, maza da mata kuma alal akalla ana iya cewa suka yi musu rikon sakainar kashi.

To amma a kasashen musulmai wadanda al'umma da gwamnatocinsu suka kasance suna bin ka'idojin Musulunci, akwai karancin afkuwar keta alfarmar mata, rashin kunya, shika da sauran muggan ayyuka. Ginshikin iyali yana da karfin gaske, mataye ba sa da sauran tsoro kana kuma suna cikin aminci wajen yawo a kan tituna da kasuwanni.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next