Hijabi Lullubin Musulunci



Kana kuma a lokacin da ta tsarkaka kuma ta samu kiyayewa irin ta hijabi, to al'umma ma za ta tsarkaka. Hakika za a iya magance da yawa daga cikin bala'o'i da cututtukan da suka addabi kasashen Yammaci, shaye-shayen giya da kwayoyi, zinace-zinace da sauran matsaloli, idan har aka bar mata suka fahimci akidar hijabi. A wadancan al'ummai, ana kula da kwakwalen mutane da kuma zaluntar samuwarsu da kuma hana su isa zuwa ga kamala, kamar yadda aka halicce su. Wadannan lalatattun al'umma da kuma shuwagabanninsu sun gano hanyar cimma wannan buri na su, don haka sai suka lalata mata, kuma ta haka ne sai suka sami damar lalata al'umma.

6- Gudummawar Mace A Wayewar Musulunci.

Hikayoyi Da Misalai : A shafuffukan da suka gabata mun ga matsayin Musulunci dangane da mace da kuma hijabi. Hakika tabbataccen ra'ayi ne. To amma hakan ya tabbata? Ya ya mace, a tarihin Musulunci, ta gudanar da ayyukan-ta, kana kuma wace gudummawa ta bayar wanda ke nuna irin babban matsayin da Musulunci ya bata yayin da ta fita daga zaluncin lokacin jahiliyya, kana ta rungumi hijabin Musulunci? A shafuffuka masu zuwa, za mu yi dubi ne a aikace na wasu mataye wadanda suka tsinka sasarin bauta ga mazaje, kana suka dauki bautar Ubangiji, Allah Madaukakin Sarki. Hakika Musulunci da kansa, ya tabbatar da irin hikimar da ke cikin dokokinsa, kuma suka ci gaba da zama wasu matakala na shiriya zuwa ga madaukakiyar rayuwa wacce take cike da kyautatawa da samar da sakamako mai kyau, samun kyawawan dabi'u, tsira da kuma tsarkaka.

Tun da hasken Musulunci ya bayyana ne a Jazirar Larabawa, mace musulma ta sami damar kade kurar wulakanci da bauta kana kuma ta yi ban kwana da ranakun zalunci da kuma bisine 'ya'ya mata da rai. Inda ta fara rayuwa irin wadda wahayi da kuma dokokin Allah Madaukakin Sarki suka tsara. Kana ta fara taka rawa cikin aikin gina madaukakiyar al'umma wacce Manzon Allah (s.a.w.a.) yake kula da ita.

Don haka, 'yan'Adam suka gano irin wannan sabon yanayi wanda ya haskaku da hasken annabci. Wannan hanya wadda wata mace wato Khadija bint Khuwailid, shugaban iyayen muminai, ta fara zabenta. Inda ta ba da dukkan dukiyarta don gudanar da dukkan ayyukan wannan da'awa, yayin da Annabi (s.a.w.a.) yake gwagwarmaya da masu bautan gumaka na lokacin Jahiliyya. Hakika ma dai, irin wannan taimakon kudi na wannan mace madaukakiya a wancan lokaci ya kasance mafi girman makami na fada tsakanin shiriya da kuma bata (gaskiya da kuma karya). Hakika wannan madaukakiyar mace ta fuskanci da yawa daga cikin wahalhalun rashin abin duniya ne saboda irin ci gaba da tayi na taimakon da'awa zuwa ga gaskiya da kuma da'awar wannan mai ceto, Annabi Muhammadu (s.a.w.a.); da kuma irin tsayuwar dakan da ta yi a kan imani da kuma kare wannan sako da kuma wanda ya zo da shi. Tun daga farkon da'awar, ta kasance a gefen Manzon Allah (s.a.w.a.), tana mai bashi taimakon dukiya, kana da taimako mafi muhimmanci na karfafa shi, soyayya da kuma tausayi ga wannan "Rahama ga Talikai". Ita ce ta farko da ta yi imani da shi, kare shi da dukiya da matsayinta, kuma ita ce ta karfafa shi da kuma kwantar masa da hankali a lokuta mafi wahala na rayuwarsa.

Amirul Muminina, Imam Ali (a.s.) a daya daga cikin huduboninsa a littafin Nahjul Balaga yana fadi dangane da matsayinta cewa: "...a kowace shekara ya (Annabi) kasance yakan zauna a kogon hira na wani lokaci, babu wani wanda yake tare da shi sai ni. Babu wani wanda zai ganshi ko ya ji shi ko kuma ya kusace shi sai ni. A wancan lokaci babu wani musulmi daga Annabi (s.a.w.a.) sai matarsa Khadija, sai kuma ni na ukunsu. A duk duniyan nan babu wani wanda ya karbi Musulunci. A wasu lokuta a wancan lokacin nakan ga hasken wahayi kana na kan ji kamshi mai dadi irin na annabci"[19]. Sauran matayen Annabi (s.a.w.a.), bayan rasuwar Khadija (a.s.), su ma sun sami Wani babban matsayi cikin tarihi. Ba za mu taba mancewa da irin gudummawar Ummu Salama wacce ta haddace da yawa daga cikin hadisan Manzon Allah (s.a.w.a.) ba. Hakika irin kauna da biyayyarta ga gaskiya da kuma hanya madaidaiciya, shahararren abu ne a cikin tarihin Musulunci inda har wasu daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s.) sukan bata amanar abubuwan da suka gada na annabci yayin da suke cikin mawuyacin yanayi.

Lalle irin gudummawar mata a tarihin zamantakewa da siyasar Musulunci yana da muhimmanci gaske. Daga cikin shahidan farko na Musulunci akwai wata mace mai suna Sumayya, matar Yasir, wacce aka gana mata tsananin azaba inda daga karshe ta kasance wacce ta fara yin shahada a Musulunci. Hakika za a iya ganin gudummawa da zaluntakan mata musulmai a shafuffukan tarihi. Wadannan mataye irin su Sumayya suna da madauka-kiyar daraja. Irin gudummawar da suka bayar ga al'amurran addini da siyasa sun zama darussa ga mataye a duk duniya wajen dawo da mutuncinsu da suka rasa.

Daga cikin irin misalin karfin da Musulunci ya ba wa mataye a farko-farkon tarihi, ita ce wata mace da ake kira Nusaiba wacce take zaune a birnin Madina. Ta kasance Ba'ansariya (mutanen Madina wadanda suka taimaki musulman da suka yi hijira daga garin Makka) ce ana kiranta da Nusaibatu Jarrah. Ta yi aure, sannan tana da 'ya'yaye guda biyu, masu suna Amarah da Abdullah. Sunanta ya fara fitowa ne a cikin tarihi yayin wata bai'a da wadansu Ansarawa, mazaje guda sittin da mataye guda biyu, suka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a.) bayan da suka karbi Musulunci. Wannan bai'a ana kiranta da Bai'atul Akbah.

Manzon Allah (s.a.w.a.) wanda yake tsananin girmama mata, yayin wannan bai'a sai ya sanya hannunsa cikin kwano cike da ruwa kana ya mika wa wadannan mata, inda su ma suka yi hakan. Wadannan mutane sun taimaki gwamnatin Manzon Allah (s.a.w.a.) matukar taimako. Domin mijin wannan mata Sumayya ya yi shahada a yakin Badar, kana daya daga cikin 'ya'yayenta ma ya yi shahada a wannan lokacin.

Hakika tarihi ya nuna mana irin yadda wannan mace Nusaiba ta kasance a wurin yaki tare da Manzon Allah (s.a.w.a.) a matsayin likita. Ta yi musharaka cikin yakukuwa da daman gaske, tana dauke da jakar ruwa, inda take yin magani ga marasa lafiya da wadanda aka ji musu rauni a filin daga.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next