Hijabi Lullubin Musulunci



To a nan wani tsari ne ya fi? Shin za mu zabi takaitaccen 'yanci ne, wanda daga karshe yake haifar da rugujewa da rashin samun nasara, ko kuma tsarin da ke kai wa ga kiyaye al'umma, sannan wanda yake kare namiji da mace ba tare da nuna wani bambanci ba? Masana kimiyya ta hanyar binciken rayuwar dan'Adam sun gano cewa, an halicci mutum da wasu sha'awoyi guda biyu:

(A)- Su ne sha'awoyin da suke bijirowa da kansu ba tare da tasirin wasu abubuwa daga waje ba, kamar sha'awar abinci, sha'awar nuna kansa ga sauran mutane da kuma sha'awar mallaka da dai sauransu.

(B)- Su ne sha'awoyin da duk da suna nan tare da mutum, to amma ba sa bijirowa sai wasu abubuwa daga waje sun motsar da su. Daga cikin muhimman irin wadannan sha'awoyi, akwai: Sha'awar jima'i, wanda wakoki da littattafan batsa da tsiraici da dai sauransu suke haifar da ita.

Musulunci, wannan addini na Ubangijin talikai, Mahalicci, Masanin kome, yana da cikakkiyar masaniya kan mafi karancin al'amurran da suke tankwara dan'Adam da kuma hatsarin da ke tattare da rayuwar mutum a duk lokacin da ya ketare haddin da aka sanya masa. Wanda idan da zai bi shi, da zai samu daman daidaita wadannan sha'awoyi a duk bangarorin rayuwarsa.

Saboda masaniyar Musulunci kan wadannan al'amurra ne, ya sa ya haramta motsa wadannan bakaken abubuwa da suke motsa sha'awa. Don kiyaye wannan bukata, Musulunci ya sanya wadansu tsarurruka na zamantakewa, tattalin arziki da siyasa. Wadannan tsarurruka sun haifar da kyakkyawan yanayi na yarda tsakanin wadannan bukatu na cikin dan'Adam da kuma bukatun sauran jama'a da kuma al'ummar da yake raye a ciki.

Wannan tsari na Musulunci kan hijabi da kuma kyautata alakar da ke tsakanin namiji da mace, an gina shi ne a bangare guda don kiyaye daidaituwan da ke tsakanin bukatuwan mutum da kuma babban burinsa na tsarkake da kuma kiyaye alakar da ke tsakanin wadannan jinsuna guda biyu a daya banga-ren. Don haka, hijabi ya kasance wani asasi ne da ke da alaka da yanayin rayuwar dan'Adam, bugu da kari kan kiyaye kyawawan dabi'u kana kuma tsarkaka da kuma tsara rayuwar al'umma dai-dai da koyarwar Musulunci.

Musulunci, ta hanyar tsara hijabi ga mata, ya takaita yanayin alakoki tsakanin wadannan jinsuna biyu ta mafi kyan tafarki. Kana ya tafiyar da namiji da mace gaba dayansu, yana mai takaita ayyuka ga kowane daya daga cikinsu don gudanar da su yadda ya dace. A al'amarin hijabi ne kawai aka bambance mace da namiji, to amma a sauran ayyuka, daya suke.

Hakan kuwa ba wai yana nuna cewa gudummawar maza da na mata a al'ummar musulmai dai-dai yake ba, lalle ba dai-dai suke ba. Shi namiji shi yake daukan nauyin kula da gida ta hanyar amfani da dukiyarsa wajen samar da abinci, matsuguni, sitira, kula da lafiya da dai sauran abubuwan jin dadin iyali. Mace kuwa tana da 'yancin neman kudi da kuma sarrafar da shi yadda take so, to amma ba hakkinta ba ne ta ciyar da gida.

Hakkin mace musulma ne kulawa da kuma tarbiyyantar da 'ya'yayenta da kuma samar da kyak-kyawan yanayi na ci gaba da daukakar iyali. Hakika hijabi yana da amfani ta bangaren iyali da kuma ga al'umma. Domin a gidan da ake girmama hijabi da kuma sanya shi, za mu ga iyalan gidan suna nuna tausayawa, taimakawa da kuma neman zaman lafiya tsakaninsu. Kana a dalilin rarraba wadannan jinsuna biyu, za a iya magance aikata laifuffukan zinace-zinace wanda ya zama ruwan dare a al'ummar kasashen Turai, inda zina tsakanin 'yan gida guda (misali wa da kanwa ko kuma kani da yarsa) ya zama jiki.

Hijabin Musulunci ba wai kawai ya takaita da rufe jiki ba ne. A'a shi wani lullubi ne da yake aiki a matsayin abin da ke nisantar wa daga aikata duk wani laifi da sabo wanda ke lalata mutum da kuma al'umma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next