Hijabi Lullubin Musulunci



Kana kuma a fili yake cewa sha'awoyin maza da mata na jima'i suna iya tashi ne ta hanyoyi daban-daban. Mace, a matsayinta na halitta mai taushin zuciya, tana bukatuwa da shafa jikinta wajen tayar mata da hankali. A daya bangaren kuma shi namiji halitta ne mai kaurin jiki da karfin sha'awa, hanka-linsa na iya tashi ta hanyar kallo kawai. Don haka mace take rufe jikinta don kada ta nuna jikinta kana shi kuma namiji ba zai ga wani abu da zai tayar masa da hankali ba. Madalla da Musulunci da ya zaba wa al'umma hijabi! Hakika ya yi dai-dai da irin yanayin mace!.

A saboda la'akari da wannan al'amari na jan han-kali, za mu ga kuma Musulunci ya haramta abubuwa kamar su luwadi ga mazaje da kuma madigo tsakanini mataye, domin kowane guda daga cikin wadannan dokoki guda biyu yana da abubuwa da yake haifarwa da kuma dalilansa, kamar yadda sauran dokoki na shari'a suke da nasu dalilan da suka dogara da su. Wadannan su ne manyan abubuwan da aka lura da su wajen kafa wannan doka; wato ta hijabin Musulunci.

5- Shubhohi Kan Hijabi.

Tambaya a nan ita ce dai: shin masu inkarin ci gaba (kasashen Turai) za su iya yarda da hijabi tattare da irin fahimtar da suka yi masa na cewa shi wani kokari ne na mayar da mace baya da kuma raunanar da ita daga tawaye ga zaluncin da ake mata, wanda hakan raunana rabin al'umma ne?

Hakika, wannan mummunar fahimta ta faro ne daga irin yadda wasu masana da 'yan siyasar kasashen musulmai suke nuna hijabi wanda ya saba wa 'yancin mace da kuma kange ta daga cim ma burinta na yin kafada-kafada da mazaje cikin ayyukan gina kasa.

Wannan al'amari yana bukatar da a fahimci tushen matsalar, ita ce kuwa: shin su wadannan masu ikirarin ci gaba da gaske suke yi yayin da suke yada wannan jita-jita? Shin me suke nufi da " 'yancin" mata? Idan har abin da ake nufi shi ne 'yancin fadin albarkacin baki; mutum ya fadi

ra'ayinsa, 'yancin mallaka; 'yancin zaben mijin aure da kuma 'yanci cikin ayyukan yau da kullum da dai saurans; to ai a Musulunci babu wani abu da ya hana ta wannan 'yancin da kuma makamantansu!

Shin hijabi ya hana mata musharaka cikin bangaro-rin rayuwar yau da kullum da kuma neman ilimi ne? Shin hijabi ya hana mata fadin albarkacin bakinsu ne? Shin hijabi ya shiga tsakanin mace da kuma hakkinta na mallakan dukiya ne? Yana da kyau a tambaya cewa, shin tun asali hijabi yana da wata alaka da wadannan tambayoyi ko kuma shi wani al'amari ne wanda yake da alaka da irin sa tufafin mace, mutunci da kuma irin kyakkyawan alakarta da wadanda suke tare da ita.

Sannan kuma wannan al'amari na hijabi ya shafi al'amurran tattalin arziki da kuma samar da abubu-wan bukatuwa ne. Domin irin hasarar da ake yi a fili take. A bisa misali mu dauka cewa akwai asasai guda biyu na samar da abubuwa: Na farko yana da alaka da ma'aikata mata, wadanda suke sanya hijabin Musulunci kana kuma suna mu'amala da mazajen da ba muharramansu, ba mu'amala irin wadda Musulunci ya yarda da ita.

Na biyun kuma yana da alaka da ma'aikata mata wadanda suke sanya tufafi masu janyo hankali, kana suke bin irin tafarkin Turai wajen mu'amala da mazaje. To hakika, za mu ga cewa asasin da ke kulawa da hijabi sai ya fi kokari da kuma samar da abubuwa da ake bukata, saboda irin alakar da ke tsakanin maza da mata. Kana, a daya bangaren kuwa, za mu ga cewa a daya asasin (asasi na biyu), wanda lalata da munanan ayyuka suke kan gaba, ana bata lokaci mai yawan gaske wajen mu'amaloli na neman biyan bukatun sha'awa (jima'i). Kana mu dauka cewa akwai dakunan karatu guda biyu: A na farkon ana kula da mu'amalolin samari da 'yan mata kamar yadda Musulunci ya tsara.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next