Hijabi Lullubin Musulunci



zuwa ga Allah gaba daya, Ya ku Muminai!, tsammaninku ku sami babbar rabo". Surar Nuri: 24:30-31. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, kana tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu (S.A.W) da Mutanen gidansa tsarkakku (A.S).

B- Kalmomin Da Aka Yi Amfani Da Su A Wannan Bincike

Lullube mata a zamanin Jahiliyya: Wato kange mata daga musharaka cikin rayuwar al'umma da kuma hana ta 'yancinta. Hijabin Musulunci: wato irin sanya tufafin da Musulunci ya yarda, wanda yake rufe dukkan jikin mace, amma ban da fuskanta da tafukanta.

Mahram: Muharrami yana nufin 'yan-'uwan mace da namiji wadanda aure ya haramta a tsakaninsu, kamar iyayen mutum, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, kawunnai,gwaggwannai, dan dan-'uwa ko 'yar'uwa, 'yar dan'uwa ko 'yar'uwa, kakan-ni, jikoki da sirikai.

Ajnabi ko Ajnabiyah (jam'insu shi ne ajanib ko ajnabiyat): Su ne wasun wadancan da aka ambata a sama wadanda aure ya halalta a tsakaninsu, misali 'ya'yan kawunnai ko gwaggwannai, ko kuma sauran dangi da bare. Ko kuma su ne wadanda babu wani haramci na Shari'a kan auratayya tsakaninsu.

1- Hijabin Musulunci: Yanayi Da Kuma Ma'anarsa

Hakika an cutar da mace ta manyan hanyoyi guda biyu, wadanda hakan su ne manya abubuwan da suka haifar da keta, wahala da zaluncin da suka faru gare ta cikin tarihi. Abu na farko shi ne irin ganin da ake yi wa mace a matsayin wata wulakantacciyar halitta da maza kan mallaka don biyan bukatunsu na jima'i, kana a dai-dai wannan lokaci kuma ita ba wata aba ba ce face kawai wata na'ura ta haifuwar yara. Kana kuma ana kwatanta ta da cewa wata rumbu ce ta ajiye gudan jini. Kana wasu siffofin da ake fadi game da mace suna nan kamar haka: ana ganinta cewa shaidan ce cikin rigar dan'Adam, ko kuma hanya ta rashin biyayya a rayuwa….da sauransu. To amma babbar manufar duk wadannan abubuwa ba kome ba ne face kawai a wulakanta ta, bautar da ita da kuma kwace mata 'yanci da hakkokinta, kana da kuma kange ta daga musharaka cikin al'amurran yau da kullum.

Hakika, tarihin mace yana cike da surorin irin azabtarwa, wahalhalu da zaluncin da ya faru gare ta kamar yadda za mu yi cikakken bayani nan gaba. Abu na biyu kuwa shi ne, ana ganin mace a matsayin wani abu ne kawai na jin dadin jima'i da kuma ribar duniya. Wannan mahanga kuwa ya samu asali ne daga irin al'adu da wayewa da ci gaban mai tonon rijiya na kasashen gabashin duniya (Turai). Domin idan har tsohon mahangan da ake wa mace na ganinta a matsayin wata wulakantacciya, kana mara wayewar halitta, wacce aka zalunta ta hanyar kwace mata 'yancinta, to ita kuwa sabuwar jahiliyyar wannan zamani sai ta yi mu'amala da ita ta hanyar da ya haifar da lalacewa da 'yancin zina ga mace. Hakika an yi amfani da hanyoyi daban-daban wadan-da suka hada da hanyoyin wayar da kai, makarantu, gidajen sinimomi, hanyoyi na dabara, dokoki, wasu tsare-tsare na siyasa na Turai da kasashen gabashin duniya don dasa wannan mahanga da kuma karfafa ta. An bi hanyoyi da matakai da dama wajen yada zinace-zinace, wanda hakan ba wai kawai ya tsaya ga zubar da mutunci da kimar mace ba ne, a'a, har ma da lalata al'umma da kuma zubar da kimar dan'adam a irin wadannan al'ummomi.

Sannan daya daga cikin abubuwan da wannan al'amari yake haifarwa shi ne yaye mace da tura ta zuwa ga zinace-zinace ba tare da la'akari da kunya ko kuma wata doka ta Ubangiji ba. Hakika wadannan irin zalunce-zalunce da wahal-halu da kuma zubar mata da kima da mutunci ya samu asali ne daga hanyoyi guda biyu: Hanyar Tsohuwar Jahilliya da kuma ta Sabuwar Jahiliyyar wannan zamani.

Lalle cikin tarihi, mace ba ta yi sa'a da kuma gamon katar da wani sako ko addini da ya kare mata mutuncinta, daidaitawa da kuma kiyaye matsayinta cikin al'umma ba, face addinin Musulunci, wannan sako na Allah Ta'ala, Ubangijin talikai. Don haka hijabi, kamar yadda wannan addini ya yi umurni da shi, ya kasance daya daga cikin hanyoyin tabbatar da irin wannan kulawan ta Ubangiji ga wannan madaukakiyar halitta kamar yadda za mu gani nan gaba.

2- Ka'idoji Biyu Kan Hijabi Mace.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next