Hijabi Lullubin Musulunci



Kana za mu ga irin tasirin da Musulunci yake da shi a kan jama'a kana shi kuma hijabi a kan mata, idan muka yi la'akari da abubuwan da suka faru a kasashen Azarbaijan da kuma Bosniya Hazgovina.

Musulunci ya bayyanar da kansa a cikin su kana kuma ya ba su jaruntaka da karfin jure wa zaluncin da ya mamaye su. Tun shekaru da dama tsarin kwaminisanci da Gurguzu ya cire musu tsarin Musulunci daga al'adunsu. Suna kiran kansu musulmai to amma sun jahilci dokoki da tsare-tsaren Musulunci. Lokacin da suka sami 'yancin kansu daga wannan tsari da babu Allah a ciki, sai suka juya zuwa ga hasken gaskiya, kana suka karbo abin da da suka rasa. Babu shakka, daya daga cikin alamun hakan shi ne yin hijabi ga mata.

Wadannan misalai suna ba da tunanin irin abin da matayen musulmi masu bin dokoki da ka'idojin Musulunci za su iya cimmawa. Suna nuni da irin babbar gudummawar da ta bayar ga rayuwar al'um-ma, wanda ya saba wa irin wadancan munanan tuna-nunnuka da kuma ra'ayoyi na wadanda suka jahilci Musulunci da kuma irin tabbatacciyar karfinsa na ruguza kangin da yake hana mata musulmai gudanar da ayyukansu karkashin inuwar ci gaban Musulunci.

7- Abubuwan da Alkur'ani Da Kuma Hadisai Suka Fadi Kan Mace Da Kuma Rayuwa: Neman Izini:

" Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku shiga gidaje wadanda ba gidajenku ba, sai kun sami izini, kuma kun yi sallama a kan ma'abutansu. Wannan ne mafi alheri a gare ku, tsammaninku, za ku tuna". (Surar Nur, 24: 27) Yin Kama Imam Ali (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Allah Ya la'anci mazaje masu mai da kansu kamar mata, ko kuma matan da suke mai da kansu kamar maza". 1- Bihar al-Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 79, shafi na 64, Ibn Dawud, Tirmizi, Nisa'i, Bukhari da Ibn Majah duk sun ruwaito shi.

Shafa Turare Yayin Fita Waje

Imam Husaini (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Duk macen da ta shafa turare sannan ta fita wajen gidanta, Mala'iku suna la'antanta kana ana debe mata albarkar Ubangiji har sai ta dawo gida". (Al-Kafi, juzu'i na 3, shafi na 74). Mummunan Kallo Imam Husaini (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Mummunan kallo daya ne daga cikin kibiyoyi masu guba na Shaidan, kana mummunan kallo yana haifar da mummunar nadam". (Kamar na sama, shafi na 82) Nesantar Abubuwan Haramun: Imam Bakir (a.s.) yana cewa: "A ranar kiyama, dukkan idanuwa za su yi kuka, in banda guda uku: idon da yaki

barci don gadin musulmai (dukiyoyinsu, kasarsu da dai sauransu), saboda Allah; kana da idon da ya yi kuka don tsoron Allah; da kuma idon da aka rufe shi daga kallon abubuwan da Allah Ya haramta"(- Mishkat al-Anwar, shafi na 155). Kallon Mata An tambayi Imam Sadik (a.s.) kan ko ya halalta ga namiji ya kalli fuskan macen da yake son ya aura, kuma ya kalle ta ta baya. Sai ya ce: "Na'am babu laifi ga namiji ya kalli fuskar macen da yake son ya aura da kuma kallon ta ta baya"( Al-Kafi, juzu'i na 3, shafi na 63). Gaishe Da Mata Imam Husaini (a.s.) yana cewa:

"Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yakan gaishe da mata, kana su ma sukan mayar masa da sallamar tasa. Kana Amirul Muminina, Imam Ali (a.s.) shi ma ya kasance yakan yi sallama ga mataye, to amma ba ya son ya gai da budurwaye daga cikin matayen, inda yake cewa: "Ina tsoron kada muryarta ta yi min tasiri, har ya kai ni ga aikata zunubi maimakon samun lada"( Kamar na sama, juzu'i na 1, shafi na163) . Azabar kallon Mata Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Wata rana wani saurayi Ba'ansare ya gamu da wata mace a garin Makka. A wancan lokacin, mata sukan sanya lullubi, sai ya fara kallonta tun tana zuwa. Lokacin da ta wuce sai ya ci gaba da kallonta, har sai da ta shiga wani lungu. Kana ya ci gaba da kallonta yayin da yake wucewa ta lungun, har lokacin da wani kashin da ke jikin garu ya kwarzane shi a fuska, inda daga nan macen ta bace masa.

Kwatsam sai ya ga jini yana zuba masa. Daga nan sai ya ce: Dole ne in je in sanar da Manzon Allah (s.a.w.a.) wannan abu da ya faru. Lokacin da Annabi (s.a.w.a.) ya gan shi cikin wannan hali sai ya tambaye shi me ya faru ne. Sai ya gaya wa Annabi (s.a.w.a.) duk abin da ya faru. Nan take sai Mala'ika Jibril (a.s.) ya sauko da wannan aya: "Ka ce wa muminai maza su runtse idanuwar-su, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa"( Wasa'il al-Shi'ah, juzu'i na 9, shafi na 63. Ayar kuma ta na cikin Surar Nur ne aya ta 30.) Zaman Gefen Titi Abu Sa'id al-Khudri yana cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku guji zama a gefen titi",sai wasu sahabbai su ka tambaye shi cewa: "Ya Manzon Allah! Ba za mu iya barin zama a gefen titi inda muke tattauna abubuwan daban-daban ba". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce musu: "Idan ba za ku iya barin hakan ba, to ku ba wa titin hakkokinsa". Sai suka ce: "Menene hakkokin titin". Sai yace: "Su ne ku rufe idanuwanku; ku nisanci cutar da sauran jama'a; ku amsa sallama; kuma ku yi umurni da alheri, kana ku yi hani da sharri"( Sahih Bukhari, juzu'i na 7-9, shafi na 63). Kwadayin Daukakan Muminai: Amirul Muminina (a.s.) yana cewa: "Lalle Allah Yana fushi da daukakar masu imani maza da masu imani mata. Saboda haka tilas mai imani ya yi fushi (da daukakar da yake samu), saboda wanda bai yi fushi da daukakar da ya samu ba, shi ne mai juyayyiyar zuciya"( Mishkat al-Anwar, shafi na 236 .(Falalar Kawar Da Idanuwa: Abu Imamah yana cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Musulmi shi ne wanda yayin da ya kalli mace kyakkyawa sai ya kawar da idanuwansa, Allah Zai ba shi ladar ibadar da dadinta a zuciyarsa take" (Al-Targib wa al-Tarhib min Hadith al-Sharif, juzu'i na 3). Kiyaye Kai Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku kiyaye kanku daga abubuwa guda shida, ni kuwa zan lamunce muku aljanna; idan za ku yi magana, ku fadi gaskiya; in kuka dauki alkawari, to ku cika; ku rike amana; ku kare farjojinku (sai ga matayeku); ku kawar da idanuwanku (daga kallon haram); kana ku kame hannayenku daga aikata zalunci da kuma abubuwan haramun (Kamar na sama, shafi na 35) Girmama Mace Yayin da yake jawabi wa musulmai lokacin aikin hajjin ban-kwana, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya gargade su dangane da abubuwan da yake tsoron za su bar su bayan rasuwarsa, inda ya ambaci mace a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwa. Ya na cewa: "Ku ji tsoron Allah dangane da mata, kana ku kula da su da kyau.( Tuhaf al-Ukul an Aali al-Rasul na al-Harrani, shafi na 23).

Aure Mai Albarka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next