Mene ne Auren Mutu'aAkwai Magana ta uku wacce ake cewa auren Mutu'a shafaffene saboda babu Gado a ciki. Wanda maganar da ta gabata ta isa jawabi Hakanan matar da take "Kitabiyya" (wacce take bin wani Addinin da aka saukar ba Musulunci ba, kamar Kiristanci, Yahudanci) idan ta auri Musulmi, bazata gaje shi ba, kuma duk da hakan tananan dai a matsayin ta na matarsa, da sauran abubuwa da hukunce-hukunce. Sannan kuma ma dai yawan maganganu akan shafe hukuncin auren Mutu'ar kansa dalili ne dake nuna rashin tabbatar shafewar.. Kuma har wala iyau sassabawar su a cikin shi kansa lokacin da aka shafe din na kara shaida hakan. Misali: · Wasunsu sukace: An shafe hukuncin ne, kuma Manzon Girma (Sallallahu alaiHi wa Alihi) ya hana ne a lokacin shekarar Yakin Khaibara. · Wasu suce: Hanin yazo ne a lokacin shekarar Budi (Amul-Fat-hi) . · Wasu suce: Ta kasance anayi, sai dai an hana ta ne a Yakin Tabuka. · Wasu suce: anyi umarnin yinta lokacin Hajjin Ban-kwana (Hajjatul-wada' i), sannan daga baya aka hana. · Wasu suce: An halasta sannan aka haramta, aka sake halastawa aka haramta, aka halasta aka haramta.
|