Mene ne Auren Mutu'a



1-    ….. Daga Jabir, yace: "Mun kasance muna auren Mutu'a, a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi), da zamanin Abubakar, sannan daga baya Umar dan Haddabi ya hana ….. (Sahihul-Muslim: 4/131, Musnad na Ahmad: 6/405, Fat-hul-Bari: 9/149).

2-    ….. Daga Ibn Abbas: Hakika Ayar Mutu'a hukuntacciya ce ba shafaffiya ba.. (Al-Kasshaf: 1/498, Al-Ghadir: 6, Al-Khazin: 1/358).

3-    ….. Munyi Mutu'a a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) da zamanin Abubakar da rabin zamanin Umar dan Haddabi sannan daga baya Umar dan Haddabi ya hana mutane yi. (Bidayatul-Mujtahid i: 2/58, da Al-Ghadir: 6/223 da 207).

4-    ….. Daga Al-Hakim, da Ibn Juraih da wasunsu, sunce: Aliyyu yace: da ba don Umar dan Haddabi ya hana yin auren Mutu'a ba da babu wanda zai yi zina sai "Shakiyy" wato ma'ana sai "Kalil" wato mutane kadan, a wata fassarar kuma akace sai dai Dan iska, amma waccen fassarar ta "kadan" tafi karfi. (Tafsirud-Dabari: 5/9, da Tafsirur-Razi: 10/50, da Durrul-Manthur: 2/140).

5-    ….. Daga Imran dan Hasinu, yace: An saukar da ayar Mutu'a cikin littafin Allah Ta'ala, sannan wata Ayar bata sauka mai shafe ta ba, kuma Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) yayi mana umarni da yin auren Mutu'a, kuma munyi Mutu'a tare da manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi), sannnan ya Rasu bai hana mu aikata ta ba, sannan wani mutum ya fadi abin da ya so na ra'ayin sa. (Sahihul-Bukhari: 2/168 da 6/33, Sahihul-Muslim: 4/48, Sunanin-Nisa' i: 5/155, da Musnadin Ahmad: 4/426, abisa ingantaccen Sanadi).

6-    ….. Daga karshe Ibn Juraih shi kadai ya ruwaito Hadisai goma sha daya akan halascin auren Mutu'a. (Nailul-Audar: 6/271, Fat-hul-Bari: 9/150).

Hadisai da Nassosi suna tabbatar da abinda Ayoyi masu Girma suka nuna ne na halascin auren Mutu'a da dawwamamman hukuncin sa har zuwa tashin Al-kiyama. Domin kuwa haramcin ya samu ne daga Umar dan Haddabi - bawai daga manzon Girma ba (Sallallahu alaiHi wa Alihi). A irin bangare na Makarantar Sunna zai iya yiwuwa ace sun bi hani ko umarni na Halifa Umar a wannan bigire da yayi hani akan auren Mutu'a, da ace ba a sami Aya ko Hadisi da yake umarni akan halascin sa ba. Amma samuwar Aya da Hadisai barkatai sun yanke musu hanzarin riko da wannan hani na sa, domin kuwa karo ne da Kur'ani da Hadisin wanda shine mai isar da wannan sako na Musulunci, wato Annabi Muammad (Sallallahu alaiHi wa Alihi). Don kuwa hakika wasu tarin Mutane daga Sahabbai da Tabi'ai kai har ma da Abdullahi dan Umar, da Halifa Umar dan Haddabin kansa sun cigaba akan halascin auren Mutu'ar ba haramcin sa ba.

MAGANA TA BIYU
SHIN AN SHAFE HUKUNCIN AUREN MUTU'A?

Malamai da daman gaske na Makarantar Halifofi (Ahlus-Sunna) sun tafi akan an shafe hukuncin auren Mutu'a, don tabbatar da matsayin Halifa na biyu Umar dan Haddabi. Wasun su suka ce: an shafe hukuncin Mutu'a daga Kur'ani mai tsarki, wasu kuwa suka ce: an shafe ta ne da Sunnar Manzon tsira (Sallallahu alaiHi wa Alihi), sai bangare na biyu suka saba akan maganganu masu yawa:

Amma maganar su da suke cewa an shafe hukuncin Mutu'a da Al-Kur'ani. Suna kafa hujja ne da wannan Aya da Ubangiji Madaukakin Sarki yake cewa:

"وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ, إِلاَّ عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانِهِمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ, فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاءَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ اْلعَادُون."            (المؤمنون – آية 6-7 )



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next