Mene ne Auren Mutu'a"Zan aureki zuwa lokaci kaza ABU NA HUDU
Babu wani gwargwado na lokaci na Shari'a sai dai kawai ya danganta ne da yadda sukayi yarjejeniya, mai tsaho ne ko gajere. Sai dai fa wajibi ne ya zamanto lokacin ayyananne ne babu ruwan sa da wani tsayin sa ko kankancin sa. Da za a ce ma an daura shi zuwa wani sashe na Rana abisa ayyanawa ya inganta, kamar ace zuwa Rana ta raba tsakiya ko faduwar ta. Sannan da za a ce an ma bata Sadakin da ba a san ko menene ba, auren ya baci abisa ingantacciyar Magana. Da za a kimanta lokacin da aiki, kamar sau daya ko sau biyu, in har da wani sanannen zamani ne to ya inganta. Baya kuma halatta ayi kari daga wannan lokaci (daya zuwa biyu), idan kuwa akayi to ya baci. Wasu kuwa sai suka ce: ai ya zama auren Da'imi ne kawai. (Shaikhu Dusiy ya tafi akan haka a littafinsa An-Nihayah: 491, da Kudubuddin Al-Kaidariy cikin Isbahis-Shi' ah: 419). A wata ruwayar kuma akace ya inganta. Bazai waiwaye ta ba bayan cikar sharadin da ya shardanta (sai dai idan wani akadin ne daban). (Al-wasa'il: 14/479, Bain a 25, a babukan Mutu'a, Hadisi na 4). Sai dai ita wannan ruwayar raunanna ce (ya da'ifanta ta sanadin Sahal bn Ziyad a cikin Al-Sanad). Baya daga cikin sharadin Ajali ace lallai sai Ajalin ya hadu da daura auren, amma ya halasta a kulla zuwa Wata guda hadi da Ajalin a tare ko kuma daga baya abisa sabani. Kuma ba zai yiwu ta auri wani ba a dan irin wannan tsakanin na jinkirin tsakanin kullawar da kuma tsawon lokacin. Sannan shima bazai aure ta ba sai da wata sabuwar kullawar. Kuma ba zai auri 'Yar uwarta ba kafin cikar wannan Wata dayan da karewar sa. Da zai zamo an ambaci Wata guda kuma ya kare, to wannan kullawar ta kare. Sannan da zai barta har tsawon lokacin da aka diba ya kare, to ta fita daga wannan kullawar. Kuma dole ya bata Sadakin ta. Amma anan Ibn Idris yace: "idan har hakan ya faru ne abisa rashin sani to ba sai ya biya ba. (As-Sara'ir: 2/623). ABU NA BIYAR
Shi Sadaki bashi da wani takamaimiyar ka'ida ta adadi a ganin Shari'a. Don haka yana inganta ne a bisa yadda sukayi yarjejeniya akai na yawan sa da rashin yawan sa da sharadin lallai ya zamo an san nawa ne. ko kuma an san kwatankwacin sa, ko nauyin sa, ko kuma an ganshi, ko siffar sa, kuma ana iya mallakar sa. Da za a daura auren akan abinda ba a san shi ba, ba a ganshi ba, ko abinda ba za a iya mallakar sa ba, to wannan auren ya baci. Sannan auren ya halatta a daura shi akan wata 'yar jaka ta abinci ko tafin hannu na abincin. ABU NA SHIDA
Sannan yana daga cikin Sharadi Macen ta zamo Musulma, ko "Kitabiyya" (wacce take da Addini saukakke daga Allah Ta'ala ba Musulunci ba). Amma ana da sabani akan "Bamajusiya" (wacce take Addinin masu bautar Rana), lallai zai hana ta shan giya, da cin naman Alade, da aikata abubuwa na haram. Baya halatta ayi Mutu'a da mai bautar Gunki, ko kuma "Nasiba" (wacce ke bayyana gabarta ga Ahlul-Baiti [Alaihimus-salam] ), kamar "Khawarijawa" (sune wadanda suka fita daga biyayya ga Imam Aliy [Alaihis-salam] har ta kai suna gaba da shi suna kafirta shi). Sannan bai halatta Musulma ta auri duk wanda yake ba Musulmi ba, ko kuma Mumina ga wanda ba Mumini ba. ABU NA BAKWAI
Auren Mutu'a kamar auren Da'imi yake bangaren Surukuta. Da zakayi Mutu'a da Mace, to ya haramta ka auri Mahaifiyarta ko 'Yarta kai tsaye. Idan kuma babu ta fari (Uwar) to ta biyu. Kamar yadda yake a litattafan Fikihu. Sannan baya halatta ayi Mutu'a tare da Baiwa alhalin ana auren 'Yantacciya auren Da'imi sai da izinin matar tasa. Idan kuwa yayi babu izininta, to al'amarin na karkashin yardar ta, idan ta yarda to aure ya inganta idan bata yarda ba aure ya baci. Wata fadar kuwa akace ya baci sai har da izininta tun farkon fari, abinda yafi kuwa shine ita 'Yantacciya koda anyi Mutu'a kamar Da'imi ne. (An-Nihayah: 459, Al-Mukhtalif: 7/82).
|