Mene ne Auren Mutu'a



·        Malam Raziy a cikin Tafsirinsa yace: …..Sawwadu daga cikinsu yace: Hakika Mutu'a ta kasance halas kamar yadda ta zamo. (At-Tafsirul- Kubra lil-Raziy: 3/200).

·        Hakanan Malam Abu Hayyan cikin Tafsirinsa bayan ya kawo Hadisin halascin ta yace: …. akan hakan Jama'a da dama daga cikin Ahlul-Baiti da Tabi'ai suka tafi. (Al-Ghadir: 6/222 wanda ya ciro daga Al-Istii'ab da waninsa).

Gamai son karin bayani filla-filla a wannan bangare a fikuhunce, da Tarihance, da Hadisance to ya koma ga littafin "Ma'alimul-Madrisat aini" na Allamah Sayyid Murtadha Al-Askari.

Don haka yanzu da zai zamanto mun gamsu da dukkanin maganaganu na shafewa da haramtawa, mu kawo cewa Mace da Namiji sun yi yarjejeniya akan suyi aure suka bayyana cewar auren nasu zai kare ne zuwa wani lokaci, menene hukuncin wannan alaka tasu?

Shin za ayi hukunci da haramcin ta kuma Zina ce? Ko kuwa za ayi hukunci da halascin ta? To hakika Magana kan haramcin ta wata hujja ce marar tushe marar dalili. Halasta ta kuwa shine dace wanda shine abinda Mazhabin Ahlul-Baiti (Alaihimus-salam) suke kai.

SHIN MUTU'A ZINA CE?

Amma Magana akan cewa tayi kama da zina ko Mutu'a Zina ce to lallai wani babban hadari ne, koda kuwa an shafe hukuncin halascin. Domin kuwa yana nufin ne Mai Shari'a Mai Tsarki (Ubangiji) ya halasta Zina sannan ya haramta ta. Shin Musulmi zai yarda da wannan?!

Ya riga ya gabata cewar auren Mutu'a aure ne kamar auren Da'imi, yana da Sharadai da Ka'idoji, sune: Daurin aure, da bada Sadaki, da sanya Lokaci, da Hankali, da Balaga, da rashin samun wani hanzari na Shari'a da zai hana, kamar Nasaba, ko wani dalilin ko an sha Nono tare, ko wani abu makamancin haka.. Amma a Zina kuwa ba a Daura aure, Da bashi da dangantaka da Mahaifinsa, bazai Gade shi ba, babu wata alaka ta aure, babu Idda a cikin Zina. Don haka kwatanta ma Mutu'a da Zina wata batacciyar Maganace, wanda mai fadarta ma wani Wawa ne marar tunani da dalili da son jayayya.

E, yana iya yiwuwa wasu suce shi auren Mutu'a an Shar'anta shi ne abisa domin samun wata fa'ida bangaren yasassiyar zuciya da raunananniya.

Jawabi anan shine: Ita Duniya cike take da abubuwa bayyanannu masu kyau da ke tsaye kyam wajen amfanar da dai-daikun abubuwa marasa kyau. (Misali, idan muka dauki kamar Wutar Lantarki, zamu ga anyi ta ne don wata fa'ida ga Al'umma, shine; suga Haske, su kunna Na'urori, da sauran su. Amma a bangare daban sai muga taba ta da Hannu ko Jiki kan iya aikawa da mutum Lahira nan take. To shin zai yiwu ace don wannan dalili kwata-kwata ace an hana amfani da Wutar Lantarki? Ko kuma idan muka dauki Batirin mota zamu ga ai don amfanin da aka yi shi, to yaya idan mutum ya zuba a Ido ko uwa-uba ya sha? Shin shima don haka kwata-kwata sai ace a daina yin ruwan Batir gaba daya?).

Wanda mafita a kwatankwacin wannan yanayi ba wai sai an haramta ainihin gundarin abin ba. Abin da yake kawai shine samar da wasu hanyoyi na bangaren halastawa tsakanin wadannan fitattun abubuwa masu kyau dake taimakawa ko fa'idantar da abubuwa marasa kyau. Don haka da samuwar Mai Shari'a na Musulunci (Mujtahidi) sai ya shardanta wasu sharadai na zamani na dole wajen yin auren Mutu'ar, don kubutar da wannan halascin Shari'a daga wadancan batattun.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next