Mene ne Auren Mutu'a



Hakane abinda yazo mana balo-balo na daga Nassosin Kur'ani mai Girma da Sunnar Manzon Tsira (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da Nassosin Sahabbai da TAbi'ai na tabbatar da Shari'ancin auren Mutu'a gaba daya. Da rashin tabbatar shafewar hukuncin nasa daga mafi yawan Sahabbai da Tabi'ai. Hakan ma a gurin Ahlul-Bait Tsarkaka, sune "Aliyyu" Sayyidul-Awsiya' da 'Yayayen sa Imamai Ma'asumai (Alaihimus-salam su goma sha daya) da Malaman Makarantar su ta Fikhu daya bayan daya.

Auren Mutu'a aurene halastacce ga Shar'a kamar auren Da'imi a Shari'a ta Musulunci, wanda ya dan saba a wasu hukunce-hukunce wadanda muka ambata a baya.

Amma kuma ruwayar Umar dan Haddabi ba wata abar dogaro bace wajen shafe hukuncin auren Mutu'a kamar yadda ya tabbata abaya daga bakunan su kansu Sahabbai daTabi'ai din. Wanda yana daga ciki irin raddin da dansa Abdullah yayi masa da aka yi masa tambaya akan menene matsayinsa akan auren Mutu'a, yace; halas ne. Aka ce masa me zai ce ga maganar babansa (Umar dan Haddabi) da ya haramta? Ya ce shin umarnin babana zan bi ko kuwa umarnin Manzon Allah?! (Bukhari).

HIKIMAR DA TASA UBANGIJI YA SAMAR DA AUREN MUTU'A

Yazo cikin Tarihin Malam Dabari 5/32 cewar: "..... Sun ambata cewar ka haramta auren Mutu'a alhalin ya kasance wani Rangwame ne daga Allah Madaukakin Sarki .....".

Da wannan Hadisin da wasunsa zamu iya gane ashe auren Mutu'a wani rangwame ne, da Tausayi, da Jin kai daga Ubangiji da yayiwa Bayinsa, domin ya nisanta su da aikata Al-fasha (Zina).

Mun sani cewar Ubangiji ya sanyawa Al'umma Sha'awa. Namiji yana sha'awar Mace, hakanan ma Macen tana sha'awar Namiji. Domin kuwa Allah mai Girma mai komai yana cewa:

"زين للناس حب الشهوات من النساء ......"     (آل عمران – 14)

Ma'ana:

"An kawatawa mutane son sha'awowi daga Mata"

Hakika wannan kawatawar ta zamo ne tamkar wata halitta ga Mutane wacce ba zata taba rabuwa da su ba makawar mutum yana cikin koshin lafiya. Don ta wannan bangaren kai tsaye zamu ce Ubangiji shine wanda ya sanyawa mutum wannan sha'awar. Don haka idan har kaga ta rabu da mutum sai da sababai guda biyu, imma dai mutum yabar wannan Duniyar ne ya mutu, ko kuwa bashi da lafiya ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next