Mene ne Auren Mutu'a
Da mutum zai auri 'Yantacciya da Baiwa a lokaci daya, to shi auren Baiwar yana nan ne a hannun 'Yantacciyar, ko ta yarda ko kuma ya baci abisa sabani. Sannan da zaka fara kwantawa da Baiwar to Ita 'Yantacciyar tana da zabi akan rabuwar auren ko cigaba da shi. Sannan har wala iyau bai halatta ya auro mata 'Yar 'yar uwarta ko na Dan uwanta ba sai da yardar ta, idan kuwa aka aikata to auren ya baci.
ABU NA TAKWAS
An so (Mustahabbi ne) Matar ta zamo Mumina mai kirki, kuma an ki (Makaruhi ne) ayi Mutu'ar da Mazinaciya, idan kuwa har akayi to dole ne a hana ta yin fasikanci. Amma fa baya daga cikin sharadin auren. Sannan yana daga Mustahabbi kayi mata tambaya akan halayenta gami da 'yar tuhuma, idan tana da aure sai ka rabu da ita. Sannan ba wajibi ne tambayar ta ta ba. Hakanan Makaruhi ne ayi Mutu'a da Budurwa ba tare da sanin Mahaifinta ba, idan kuwa bata da Mahaifi to Makaruhi ne kai tsaye ayi Mutu'ar da Ita. Idan kuma ya zamanto anyi to Makaruhi ne a kawar mata da Budurcin ta. Amma ba haram bane (duk da dai wasu Malaman na ganin haram ne). Sannan idan sun yi sharadi da Ita akan haka to haramun ne akansa ya kawar da Budurcin.
ABU NA TARA
Da Mushriki zai musulunta kuma a tare da shi akwai Bakitabiya wacce suka yi Mutu'a, to aurensa yananan har zuwa karewar lokacin. Sannan idan Itace ta musulunta tare da cewar ya Sadu da Ita, to yayin da ta kare Idda ko lokacin da suka diba ya kare bai musulunta ba, to sai a raba auren. Idan kuwa a cikin Idda ne ta musulunta to sai su rabu, koda kuwa bai Sadu da Ita ba zasu rabu daga yayin da ta musulunta. Idan kuwa ba "Kitabiyya" bace daya daga cikinsu ya musulunta bayan ya Sadu da Ita, to zasu jira ne har ta gama Idda ko lokacin ya kare sannan a rabu. Ko waye a cikinsu ya musulunta kafin dayan to sai a raba auren. Idan dayan yazo ya musulunta tare da cewar tana Idda ko ragowar lokacin rabuwa, to aurensu yana nan. Idan kuwa kafin ya Sadu da Ita ne, to auren ya baci nan take.
ABU NA GOMA
Wajibi ne bada Sadaki in har an daura auren. Da lokacin da aka diba zai kare kafin a Sadu da Ita to rabin Sadakin ya tafi, idan ya zamanto sai da ta bayar da Sadakin ne kana auren ya kare, to sai ya dawo mata da rabin kudin. Idan kuwa ya Sadu da Ita ne to gaba dayan Sadakin hakkin tane idan ya kare ne da lokaci. In kuma tabar wani ne daga ciki, to sai ya sanya daga cikin Sadakin kamar yadda tabar wani bangare, kuma ya danganta gaba dayan Sadakin zuwa Ajali bawai rabinsa ba. Da za ace ta hana shi kanta gaba dayan lokacin, babu Sadaki gareta, da sabanin kuma idan ta bashi kwanakin.
ABU NA GOMA SHA DAYA
Abinda yake kadai shine wajibi abisa Sharadi wajen daura auren ambatar Sadaki, da Ajali (lokaci). Abinda yake bayan wannan kuwa Mustahabbi ne ambatonsa. Misalin ya ambata mata cewar babu Nafakah babu Gado. Kuma akwai Idda a gareta bayan lokaci ya kare, da zai bar ambaton wani abu bayan ambaton wadannan Sharadi biyun to auren ya dauru. Dukkanin Sharadin da zai Shardanta yayin daurin auren, to hakika dolene bin sa ko da kuwa an kwatanta auren da abinda bazai gabatar da shi ko jinkirta shi ba. Kuma baya zama Sharadi tare da ambatonsa cikin daurin aure dawo da shi bayansa.
Kuma ya halasta a Shardanta mata lokacin da zai rika Saduwa (Jima'i) da Ita, Dare ne ko Rana, ko kuma kowane lokaci ayyananne. Idan zai Shardanta mata sau biyu ko sau da yawa a lokuta ayyanannu, to baya halasta gare ta taki. Sannan da zatayi Sharadin kada ya Sadu da Ita ta Farji, to bai halasta gare shi ya Sadu da Ita tanan din ba, da kuma zata yi masa izinin bayan sannan ya halasta abisa wata ruwayar. (Wasa'ilus-Shi' ah:14/491, babi na 36 a babin Mutu'a, Hadisi na 1).
ABU NA GOMA SHA BIYU
Dan da aka Haifa daga auren Mutu'a yana rabuwa ne ga Iyayensa biyun (Uwa da Uba), baya halasta dayansu yace ba nasa bane.. Kuma ya halasta rabuwa da Ita Matar, ba sai da izininta ba, da za a rabu da Ita din kuma tazo da Da to Dansa ne, ba kuma zai taba yiwuwa yaki karbar sa ba a matsayin don ya rabu da Uwar. Da kuwa za ace yaki karbar sa akan kansa to wannan ma ya kore shi akan ba dan nasa bane a fili, kuma bai da bukatar yin wani "Li'ani" (wato yin rantsuwa gaban Shari'a yadda Shari'a ta tsara akan kowannen ma'aurata yayi rantsuwa don karyata dayan sa akan Da).
ABU NA GOMA SHA UKU
Kamar yadda ya gabata ne cewa auren Mutu'a ba a yin Saki, sai dai yana karewa ne imma dai Mijin ya bar mata kwanakin nata, ko kuma da fitar lokacin da aka dibarwa auren. Hakanan baya yiwuwa ayi "Ila'i" (wani nau'i ne da Miji kan yi Rantsuwa akan bazai Sadu da Matar sa ba, har sai wata hudu. Idan kuma ya dawo ya Sadu da Ita lokacin bai cika ba to Kaffarar Rantsuwa ta hau kansa. Idan kuma yaki har bayan wata hudu, to anan Matar ta Saku …..), ko "Li'ani" abisa maganar da tafi karfi (Li'ani shine kamar yadda akayi bayani a baya. Kuma yadda yake faruwa shine: namiji ya jefi matar sa da zina yace Da ba nasa bane, idan aka tsayar mata da Shaidu hudu Adalai to za a yi mata Rajamu, idan kuma an gamsu da Tsinuwar da tayi akanta to sai ayi masa Bulala Tamanin, idan kuwa ba haka ba to babu Haddi akansa). Amma abinda kuma yake a sarari shine sabanin faruwar tasu.
ABU NA GOMA SHA HUDU
Ya halasta ga matar da take Baliga, mai hankali ta daurawa kanta auren Mutu'a. Bai daga cikin Sharadi ace sai da izinin Waliyyi ko da kuwa Budurwa ce (amma anan ma akwai sabanin Malamai akwai wadanda suka tafi akan wajibi ne sai sann Waliyyanta).
ABU NA GOMA SHA BIYAR
Sannan a wannan auren Mijin da matar basa gadon junansu, ko da anyi da Sharadin haka ko ba a yi ba duk daya ne. Ko da kuwa sun sanya Sharadi su biyun ko dayan su, to anan Shaikhu Dusiy yace: zasu iya gadon aiki abisa Sharadi, amma abinda yafi shine rashin hakan. Babu "Nafakah" (wahalhalu, kamar Ciyarwa, Sutura, Matsuguni na dindindin, da sauran su) ga wannan matar. Sannan ya halasta yayi Mutu'a da sama da mata hudu kai bama adadi, sun kasance 'Yantattu ko Bayi ne. amma abinda yake shi yafi kada a haura sama da mata hudu.
|