Mene ne Auren Mutu'a



Ma'ana:

"Zan aureki, ko zanyi Mutu'a dake izuwa lokaci kaza akan Sadaki kaza"

Sannan babu makawa daga "Al-Kabul", (Al-Kabul shine amincewa daga Matar da za a kulla auren da Ita akan abinda ka nema na auren da lokacin da Sadakin). Kuma yadda ake yinsa shine zata fadi dukkan abin da ke nuna yardar tane akai kamar tace:

"قَبِلْتُ اْلنِّكَاحْ أو قَبِلْتُ اْلمُتْعَةِ, وَلَوْ قَالَتْ: قَبِلْتُ أو رَضِيتُ, وَاقْتَصَرَ جَازَ, وَلَوْ بَدَأَ بِالْقَبُولِ فَقَالَ: تَزَوَّجْتُ, فَقَالَتْ: زَوَّجْتُكَ, صَحَّ"

Ma'ana:

"Na amince da auren, ko na amince da Mutu'ar, kai koda cewa tayi: na amince ko na yarda, bata kara komai akai ba ya halasta. Kuma koda da za a fara ne da "Kabul" yace: "Tazawwajtu" , tace: "Zawwajtuka" ya inganta".

Auren Mutu'a baya kulluwa da lafazin Kyauta, ko Mallakarwa, ko Haya, ko Aro.

Yana daga cikin sharadin "Al-iijabu wal Kabul" yin furuci da sigogin da suka gabata. Da za a ce: "Akbala" ko "Ardha" a kudurce manufar a zuci to auren bai kullu ba. Wasu suka ce: da zai ce:

"أَتَزَوَّجُكَ مُدَّةِ كَذَا, وَقَصِدَ اْلإِنْشَاءِ, فَقَالَتْ: نَعَمْ, أَوْ زَوَّجْتُكَ صَحَّ"

Ma'ana:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next