Mene ne Auren Mutu'aMenene ya sami irin wadannan maganganu (na umarni da hanin Mutu'a) suke fitowa a bayan zamanin Sahabbai ya shude? Don me yasa shi Umar dan Haddabi din tun lokacinsa bai yi shaida da dayan su ba yayin da ya hana Mutu'ar. Hakika abinda yake a fili shine da ya kasance a hannunsa akwai wanin wadannan Hadisan da ya kawo shi. Sananne ne cewa ya kawo wa Halifa Abubakar Hadisai na Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) Halifa na biyu (Umar dan Haddabi) bai zamo wadatacce akan haka ba, sai dai kawai yayi gaggawar hukunci ne, don kuwa Musulmi da Sahabbai basu amince da abinda Halifa Umar ya yanke ba sai ma Raddi da sukayi masa. Domin sun san zamanin Manzon tsira (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da Abubakar sarai, da ace akwai wani hani to bazai taba buyar musu ba da sun sanshi. Sannan su kansu wadannan maganganu (na an shafe) suna inkarin maganar Halifa na biyun ne kansa. Domin kuwa cewa yayi shi: "متعتان كانتا على عهد رسول الله (ص) أنهى عنهما وأعاقب عليهما متعة النساء ومتعة الØج" Ma'ana: "An kasance ana yin Mutu'a guda biyu zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) to ni na hana kuma zanyi azaba akansu, Mutu'ar Aure da Mutu'ar Hajji" (Sharhul-Ma' anil-Athar: 2/146, Malam Ahmad Bn Muhammad bn Salmatul-Azdi) . Amma sai ga shi su Ahlus-sunna din sun saki hani daya daga hani biyun da Umar din yayi sun Tabbas da ace akwai wani abu dake nuna shafewar daga Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da ya dan jona shi a maganar sa, da bai tsaya danganta abin gare shi shi kadai ba.. Don haka a Wannan maganar ma tana dada bayani balo-balo A cikin tautaunawar ta Halifa na biyu da wannan Sahabi, lokaci daya yana tabbatar da cewar haramta Mutu'a wani mataki ne da shi kadai ya zaba abisa son ran sa, babu wani dan bantare na Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi) a ciki. Sannan ijtihadin da ya bayyana na haramta ta a wannan Muhawara (Tatatunawa) ba cikakkiya ba ce, kuma bacinta bayyananne ne. Wanda shi da kansa yake ikirarin tabbas Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ya halasta ta a zamanin lalura. Kaga hakan na nuna kenan halas ce lokacin lalura. To don me ya haramta ta, ya hana yin ta, yayi alkawarin azaba ga wanda duk ya aikata ta, bai sanya haka a bisa lalurar ba?! Gashi kuwa cewar tabbas Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ya halasta ta a cikin tafiye-tafiyen sa, wanda tafiya wani abu ne daban sannan lalura ma wata aba ce daban kowanne zaman kansa yake yi.
|