Mene ne Auren Mutu'aMene ne Auren Mutu'a
Bismillahir Rahmanir Rahim
Alhamdu lillahi Lokuta da daman gaske nakan rasa gane menene To idan hakane me ke faruwa ga Shin aure ne kadai "وَاْلمÙØْصَنَات٠مÙÙ†ÙŽ اْلنÙّسَاء٠إÙلاَّ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانÙÙƒÙمْ........" Ma'ana:
"Kuma da Mata masu aure banda abinda hannuwan ku suka mallaka (Baiwa)" Malam Ibn Kathir ya fada a cikin littafinsa na Tafsiri cewa ita wannnan "Illaa maa malakat aimaanikum" ana nufin banda abinda hannuwanku suka mallaka na Fursunonin Yaki, domin kuwa su halas ne gareku, kuyi Jima'i da su yayin da sukayi Istibra'i, (yace) hakika wannan Aya ta sauka ne akan haka. Sannan yace: Malam Ahmad Hanbali (cikin littafinsa) 2/72, yace: "Munzo da Fursunonin Yaki daga Fursunonin Yakin ranar "Audas" a cikin su akwai Mata. Sai muka ki muyi tambaya akansu, akwai Mata a cikin su. Sai Annabi (Sallallahu alaiHi wa Alihi) ya tambaye mu, a take sai wannan Ayar ta sauka, aka halasta mana Farjinsu (Tafsirin Ibn Kathir: juzu'i na 1, shafi na 474). Sannan Malam Muslim ya fitar ta hanyar Sa'idu dan Abii Urwata daga Katadata daga Abil-Khalil Alkamatul-Hashimiy daga Abi Sa'idul-Khudriy, Hakika Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) ya tura Runduna zuwa "Audas" ranar Hunainu suka riski Makiya inda suka cimmasu, sukayi galaba akansu, suka kamo Fursunonin Yaki. Sai mutane daga Sahabban Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) suka zamanto abin gwasale daga masu ziyartarsu a dalilin matansu, daga ciki akwai Mushrikai. Sai Allah Ta'ala ya saukar da "Wal-muhsanatu ……" ai su halasne gareku idan sun gama Idda. (Al-Aja'ib fii bayanil-Asbab: juz'i na 2, shafi na 855). Da wadannan takaitattun Hadisai zamu fahimci cewar akwai wata alaka da Addinin Musulunci ya yarda da ita, wacce ta halastawa Namiji Saduwa da Mace, wato hanyar mallakar Baiwa. Babu wani batun daura aure sai dai kawai ka jefa ta Daki abinka. Don hakane ma ta samo suna a Hausance da (Sadaka),wato ka saka a Daki. Sannan wani abin a kula game da Sadaka ko Kwarkwara (Baiwa) shine, babu wani maganar Saki fa illa yayin da ka siyar ko ka bayar da ita (Baiwar) shine Sakinta. To kaga ashe In dai har kana kyamar Mutu'a don rashin bayyana Daurin aure a fili ne, to ya zaka ce kuma akan Kwarkwara da itama ba a bayyana Daurin auren ta bilhasali ma ita Kwarkwara babu wani Daura aure kwata-kwata a wajen mallaka?! Ko kuwa kana kyamar tane don babu Saki a cikinta? To idan haka ne yaya zaka ce kenan akan Kwarkwara da itama babu Saki a wajen rabuwa da Ita? Sakin ta shine ka sayar ko bayar da ita shike nan alaka ta kare. Idan kuwa tunanin ka ya tafi ne wajen rashin Wajabta Ciyarwa, Shayarwa, Dawwamammen Matsuguni, to yaya zaka ce akan auren Da'imi da shima wadannan hakkokin
|