Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



Don haka wadannan ayoyi guda biyu da wasu misalinsu, wace alaka suke da ita dangane da rokon da muke wa Manzo a matsayinsa na bawan Allah mai matsayi, ko kuma kawai mu kira shi ba tare da nufin ibada ba.

A cikin Littattafan masu inkarin kamun kafa da wani bawan Allah, sun tattaro duk ayoyin da suke magana danagane da mushrikai da suke kiran gumakansu na karya, sannan suka dora wadannan ayoyi a kan musulmai masu kamun kafa da ruhin manyan bayin Allah. Duk da cewa tare da la’akari da wasu abubuwa guda biyu sun fita daga bahsimmu kamar haka:

1-Wadannan ayoyi suna magana ne a kan mushrikai ba masu kadaita Allah ba.

2-Kasantuwar mashrikai sun yi imani da cewa wadannan gumakansu su suke tafiyar da wasu ayyukan Ubangiji (rububiyya) shi ya sanya kira ko rokon da suke wa gumakan ya zama ibada, amma musulmai sakamakon tsarkin imaninsu da kadaita Ubangiji suna girmama bayin Allah kuma suna kamun kafa ne da su sakamakon Allah ne ya ba da iko a hakan.

A takaice: haramta kira da aka yi a cikin wadannan ayoyi guda biyu, ya kasance ne sakamakon suna yin hakan ne a matsayin bauta, ba wai ko wane kira ko roko ba wanda yake baya tattare da wannan siffa. Domin kuwa mu gane wannan shiri na masu inkarin Tawassuli da bayin Allah, zamu ka wo wasu daga cikin ayoyin da suke kawowa a wajen bayanai da rubuce-rubucensu, ta yadda zai bayyana yadda suka yi amfani da wadannan ayoyi suka canza wannan al’amari, ta yadda suka dora ayoyin da suka sauka a kan mushrikai a kan musulmai, ga wadannan ayoyi kamar haka:

“Wadannan wadanda suke kira ba su amsa musu da komai”[18].

“Wadannan wadanda kuke ba zasu iya taimakonku da komai ba, sannan ba zasu iya taimakon kawunansu ba”[19].

“Wadannan wadanda kuke kira suma bayi ne kamar ku”[20].

“Wadanda kuke kira sabanin Allah ba su mallaki koda bawon dabino ba”[21].

“Ka ce yanzu mun kira wanin Allah wanda ba ya amfanar da mu kuma ba ya cutar da m u”[22].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next