Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



3-Sallar rokon ruwa tare dakananan yara da tsofaffi

A cikin ladubban sallar rokon ruwa ana cewa ya fi dacewa masu sallar rokon ruwa su fita tare dakananan yara da tsofi, har wasu ma suna cewa a tafi tare da dabbobi ma wajen wannan sallar rokon ruwa. Manufar kuwa zuwa dakananan yara marasa laifi da tsofaffi raunana da dabbobi wadanda ba su magana shi ne, domin suna cewa idan su ba su cancanci rahamar Ubangiji ba sakamakon zunubbansu[2].

Ya Ubangiji wadannan kananan yara mararsa laifi, da tsofaffi raunana, da dabbobi wadanda ba su iya magana, sun cancanci rahamarka.

Ya Ubangiji albarkacinsu ka aiko mana da rahamarka!

Ya uabngiji! Mai lambu saboda itaciya guda daya yake ban ruwa, amma sakamakon haka sai ciyawu ma su samu!

Wannan yana nuna mana cewa tun kafin zuwan musulunci mutane a dabi’ance sun kasance suna kamun kafa da abubuwan da suka cancanci rahamar Allah, don neman biyan bukatunsu, kuma da musulunci ya zo ya tabbatar musu da hakan.

4-Khalifa na biyu yana kamun kafa da Ammin Manzo (s.a.w)

Bukhari a cikin sahih dinsa yana ruwaito cewa Umar Bn khattab a lokacin fari da tsananin rashin ruwan sama ya kasance yana kamun kafa da Abbas dan Abdul Mutallib domin su samu ruwan sama, ga abin da yake cewa: Ya Allah muna muna rokonka albarkacin annabimmu ka shayar da mu ruwa, ya Allah muna kamun kafa zuwa gareka da ammin annabimmu ka shayar da mu sai su sha![3]

Dangane da danganen wannan hadisi kuwa babu sauran wata magana domin kuwa sahih bukhari karbabbe ne a wajen ‘yan Sunna, saboda haka magana kawai ta rage wajen ma’anarsa.

Duk lokacin da aka bai wa wani balarabe wannan hadisi wanda a cikin zuciyarsa bai hadu da wani sabani ba zai ce: Khalifa na biyu ya kasance yana kamun kafa ne da ammin Manzo domin Allah madaukaki ta albarkacinsa ya aiko da ruwan sama ya shayar da su saura su samu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next