Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



“Kada ka kira wanin Allah wanda ba ya amfanar da kai haka nan ba ya cutar da kai”[23]

Masu inkarin Tawassuli da bayin Allah a wuraren wa’azuzuwansu da rubuce-rubucensu suna kafa hujja ne da wadannan ayoyin suna dora su a kan musulmi masu kamun kafa da bayin Allah ba tare da wani dalili ba, alhali kuwa wadannan ayoyi ba su da wata alaka da tawassuli da ake yi a cikin musulunci. Masu karatu suna iya komawa zuwa ga tafsirai domin su ga dalilan saukar da wadannan ayoyi a bayyane.

Wadannan ayoyi suna magana ne da masu bautar gumaka wadanda suke da imanin cewa amfani da cutarwa, daukaka da kaskantarwa duk suna hannun wadannan allolin nasu na karya, haka nan samu nasara a wajen yaki duk yana hannunsu, ta haka ne abin da suke yi ya zama bauta, domin su samu wadannan abubuwan da suke gani suna zuwa ne daga gare su. Amma musulmi masu kamun kafa da bayin Allah akidarsu kilo mita dubu ta nisanta da wannan akida batacciya, cin nasara da kariya dukkansu suna zuwa ne daga Allah. Don haka girmamawar da suke wa ma’asumai (a.s) sam ba shi da alaka da cewa sun dauka ne su alloli ne ballantana ya zama bauta, suna haka ne domin suna ganinsu bayin Allah ne masu girma da daukaka a wajen Allah.

Mafi yawa cikin addu’o’immu muna cewa ne; “Ya Allah don matsayin Manzonka Muhammad da alayansa” wannan mastayi kuwa ya yake? Wannan matsayi kuwa shi ne matsayin da Allah ya ba su, sannan Kur’ani mai girma yana ambatar wasu daga cikin annabawa da wannan matsayin kamar yadda yake cewa dangane da annabi Musa (a.s) “Ya kasance yana da matsayi a wajen Allah”[24]. Haka nan yana cewa dangane da annabi Isa (a.s) “Yana da matsayi a duniya da lahira”[25]. Wannan shi ne matsayin da Allah da kansa ya ambata a cikin kur’ani dangane da bayinsa, wanda sakamakon haka ne suke da kusanci da matsayi a wurin Allah madaukaki.

Kalu bale na hudu: Kamun kafa yana nufin neman taimako daga wanin Allah, Mutumin da yake tawassuli a lokacin da ya shiga cikin halin kaka- na-kayi, wannan yana nufin yana neman taimako daga wanin Allah, duk da yake cewa babu wani wanda za a iya neman taimako daga gare shi sai Allah, kamar yadda Kur’ani yake cewa: “Kawai gare ka muke neman taimako”.

Amsa: wannan kuwa yana zama matsala ne ga mutumin da yake bai san wani abu ba daga Kur’ani, domin kuwa a baya mun yi bayani a kan cewa ana iya jingina aiki guda daya zuwa ga Allah a lokaci guda a jingina shi zuwa waninsa, haka nan mun kawo wurare da dama daga cikin Kur’ani da suke bayani a kan hakan, kamar misalin daukar rai ko rubuta ayyukan bayi, sannan muka yi bayani cewa wannan ba shi da wata matsala, domin kuwa jinginawa zuwa ga Allah a matsayin komai yana zuwa daga gare shi ne kuma sai da izinisa, jingina shi kuwa ga wani bawan Allah da ma’anar ya yi wannan aiki ne karkashin ikon Ubangiji.

Allah madaukai ba tare da ya nemi taimako ba daga wani wuri yake aiwatar da ayykansa, amma waninsa yana yin hakan ne tare da izinin Ubangiji, don haka aikinsa ma aikin Allah ne da wannan ma’ana.

Don haka babu matsala a lokaci guda cewa babu wanda za a nemi taimako daga gare shi sai Allah kuma a nemi taimako daga waninsa, domin kuwa neman taimako daga wani bawan Allah ba yana nufin cewa neman taimako daga gare shi maimaikon Allah. Domin kuwa yana yin komai ne da izinin Ubangiji, bisa haka ne Kur’ani yake cewa a wajen Allah kawai ake neman taimako, kuma a wani wuri yake cewa mu nemi taimako daga wanin Allah, kamar yadda yake cewa: “Ku nemi taimako daga hakuri da salla, domin kuwa suna da girma a wajen masu tsoron Allah”. [26]

Zulkarnaini lokacin da yake so ya gina bango domin ya kare mutane daga harin yajuju ga abin da yake cewa mutanensa: “Abin da Allah ya hore mini ya fi abin da zaku yi mini, don haka ku taimaka mini da masu karfi”[27]

Duniya musamman duniyar mutane ta kafu ne kan taimakekeniya, sun kuma kasance suna neman taimako da sunayen annabawa da manyan bayin Allah daga junansu, sannan sam ba su ganin wannan ya saba wa asalin kadaita Allah madaukaki, domin kuwa taimakon wanin Allah yana karkashin iko ne na Allah madaukaki, wanda ya bai wa mutum wannan damar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next