Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



Saboda haka a cikin wannan al’amari matsayin Abbas shi ne lokacin da umar yake addu’a ya yi nuni da shi inda yake cewa: “Ya Allah muna kamun kafa da ammin Manzo ka shayar da mu”

Na uku: Ibn Asir ya yi bayani yadda aka gabatar da wannan salla da addu’ar rokon ruwa, yana cewa Umar ya kasance yana nuni da Abbas yana cewa: “Wallahi wannan shi ne tsani zuwa ga Allah kuma mai tsayi a wurinsa”[4]. Ya kasance yana rokon Allah ruwa a cikin wannan hali. Don haka kamun kafa ya kasance da shi kansa Abbas ne ba da addu’arsa ba.

Ibn Hajar Askalani (ya rasu 852) a wajen sharhin wannan hadisi yana rubuta cewa: dangane da abin da ya faru da Abbas yana nuna mana yadda ya halatta mutum ya yi kamun kafa da mutanen kwarai da iyalan gidan Manzo don samu ruwan sama[5].

A karshen wannan Bahasi zamu yi tunatarwa da cewa, Tawassuli ko kamun kafa da addu’a wacce take kowa ya aminta da wannan, wani nau’i ne na kamun kafa da wanda yake addu’a sakamakon matsayi da girma da yake da shi a wajen Allah. Domin kuwa idan da mai yin addu’ar ba shi da wani matsayin na musamman a kan abin da ya shafi tsarkin ruhi, sam addu’arsa ba zata iya zama mai tasiri ba.

Kamun kafar Masu Tsarki Da Matsayi A Cikin Ruwaya

Ya zo a cikin ruwayoyi da dama na AhlusSunna dangane da kamun kafa da manyan bayin Allah tsarkaka, amma abin mamaki a nan shi ne masu sabani da wannan abu duk da cewa suna ganin wadannan ruwayoyi har yanzu suna ci gaba da wannan fito na fito nasu, a nan masu wannan akida suna koyi ne da Ibn Taimiyya ba suna koyi da gaskiya ba ne, idan da ba suna yanke hukunci ba ne tun kafin su ga dalilai tabbas da ba zasu dage ba a kan wannan akida tasu ba.

A nan zamu kawo wasu daga cikinsu:

1-Atiyya Aufi ya ruwaito daga Abu Sa’idul Kudri yana cewamanzo ya ce: duk wanda ya fito daga gidansa da nufin zai je masallaci ya yi salla idan ya karanta wannan addu’ar rahamar Ubangiji zata lullube shi, sannan mala’iku da yawa zasu yi masa addu’a su nema masa gafara a wajen Allah. Wannan addu’a kuwa ita ce: “Allahumma inni as’aluka bi hakkis Sa’ilina alaika, wa as’aluka bihakki mashai haza, Fa inni lam akhruj ashran wala batran wala rayyan wala sum’a, innama kharajtu itka’a saktik wabtiga’a mardhatika, an tu’izani minan nar, wa an tagfira zunubi, innahu la yagfiruz zunuba illa ant”

Wato, ya Ubangiji! Ina rokonka don matsayin masu rokonka, ina rokonka da matsayin wannan tafiya tawa, kuma ban fito ba don jin dadi ko saboda riya in nuna wa wasu mutane, ya Allah na fito ne domin tserewa fushinka da azabarka da neman yardarka, ya Allah ka tseratar da ni daga wuta, kuma ka gafarta mini zunubbaina don babu mai gafarta zunubbai sai kai.

Wannan hadisi dangane da ma’anar a kan abin da muke magana a kan shi na kamun kafa da masu matsayi da tsarki a fili yake. Sannan sanad ko danganen wannan hadisi ingantacce ne domin kuwa dukkan maruwaitan wannan hadisi an amince da su, sai kawai mutum guda wanda dole mu yi bayani a kansa, wannan kuwa shi ne Atiyya Aufi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next