Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



Abin mamaki a nan shi ne wadanda suke inkarin neman taimako daga wanin Allah suna ganin ana iya neman taimako daga wanin Allah a lokacin da yake raye, amma bayan ya mutu ya haramta kuma yin hakan ma shirka ne, alhalin idan abu shirka ne kasantuwar bangare guda yana da rai da bashi da rai ba ya canza wannan abu, saboda haka neman taimako daga wani idan har ya kasance muna ganin cewa yana iya yin hakan ne tare taimakon Allah sam ba shirka ba ne, wannan kuwa ya kasance yana da rai ne ko kuwa bayan mutuwarsa ne. Daga karshe zamu yi tunatarwa a kan wasu abubuwa guda uku kamar haka:

 

1-Ruwayoyin Halascin Tawassuli Ko Kamun kafa, Mutawatir Ne

Ruwayoyi da suke magana a kan Tawassuli wadanda muka kawo kadan daga Littattafan AhlusSunna kodai mutawatir ne ko kuma gab suke da su zama mutawatir, saboda haka ba zai yiwu ba ta hanyar raunana danganen wadannan ruwayoyi mu yi inkarin wannan al’amari, domin kuwa wadannan ruwayoyi suna nuni da cewa wannan al’amari ya kasance kamar ruwan dare a tsakanin al’ummar musulmi a tsawon tarihi, idan har mun kauce wa ambatar wasu da hakacikin wadannan ruwayoyi da suke magana a kan Tawassuli wadanda wasu daga cikinsu ta fuskar sanad ko dangane suna da rauni, wannan ba zai cutar da abin da muke managa a kansa ba, kamar yadda muka san cewa al’amarin haka yake dangane da hadisi mutawatir.

2-Littattafai Dangane Da Tawassuli

Al’amarin Tawassuli ko kamun kafa da bayin Allah, wani abu ne wanda yake an sallama a kansa a cikin musulunci, sakamkon haka ne manyan malaman hadisi da na fikihu sun rubuta littafai da dama a kan wannan mas’ala tun kafin Ibn Taimiyya da kuma bayansa, wadanda a nan kawai zamu kawo wasu daga cikinsu:

1-Alwafa fi fadha’ilul Mustafa Ibn jauzi (Ya rasu shekara ta 597) a cikin wannan littafi akwai babi na musamman wanda yake magana a kan kamun kafa da Manzo da neman ceto da shi da kabarinsa mai albarka.

2-Misbahuz zulam fi mutagisina bi khairi anam, wanda ya rubuta shi Muhammad Bn Nu’uman Maliki (ya rasu shekara ta 973) Samhudi a cikin littafinsa wafa’ul wafa ya ruwaito da dama daga wannan littafi dangane da Tawassuli.

3-Al-bayan wal ikhtisar, wanda Ibn Daud Maliki shazali ya rubuta, a cikin wannan littafi ya kawo yadda manyan malamai da bayin Allah suke kamun kafa da Manzo (s.a.w)

4-Shifa’us sikam, wanda Takiyyuddin Subki ya rubuta ya yi kariya da kyau a kan kamun kafa da Manzo a cikin wannan littafi nasa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next