Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



Sai Manzo (s.a.w) ya ba da umarni da a yi mata wanka sau uku, sannan ya ciro rigarsa ya ce a yi mata likkafani da ita, sannan ku yi mata lahadu (wani nau’in kabari ne) da umurnin manzon Allah, sannan shi da kansa ya shiga cikin kabarin, ya debo kasar lahadun da hannayansa, bayan ya gama wannan aiki, sai ya kwanta a cikin kabarin ya ce: Ya Allah wanda yake kashewa kuma shi a raye yake ba ya mutuwa, ka gafarta wa uwata Fadima bnt Asad, ya Allah ka fahimtar da ita hujjarka, Ya Allah ka yalwata kabrinta albakarcin girman manzonka da manzanninka da suka gabata, kamar yadda kake mafi jin kan masu Jin kai[6].

Wannan hadisi yana bayyanar da matsayin mahaifiyar Imam Ali (a.s) kamar yadda wannan hadisi yake nuna cewa ana iya kamun kafa da masu tsarki. Kawai abin da zai jawo hankalin masu sabani a cikin wannan al’amari shi ne, wani maruwaici guda daya mai suna ruh Bn Salah, duk da cewa Ibn Habban da Hakim Nishaburi wadanda suka kasance babu kamarsu a cikin ilimin hadisi a zamaninsu sun yi bayani a kan cewa wannan mutum amintacce ne. [7]

A nan zamu takaita dangane da kawo hadisai AhlusSunna, duk da cewa akwai ruwayoyi da dama da suka fi haka a kan wannan magana, amma dangane da ruwayoyin da suka zo daga Ahlul baiti (a.s) danagane da wannan nau’i na kamun kafa suna da yawan gaske, ta yadda suna da yawan gaske a cikin addu’o’in Amirul mumininna da Husain da addu’o’in Imam Zainul abidin (a.s)

Imam Husain (a.s) a cikin addua’r arfa ga abin da yake cewa:

Ya Allah muna fuskantarka a cikin wannan dare wanda ka daukaka shi ka kuma girmama shi, Allah muna kamun kafa da Manzonka Muhammad wanda shi ne fiyayyen halittarka sannan amintaccenka wajen kai wahayi.

A nan zamu yi nuni dangane da wasu kalu bale a takaice:

Kalu balanta Da Amsoshinsu

Kalu bale na farko: shi ne, wannan nau;in tawassuli ko kamun kafa bai kasance ba a lokacin sahabbai da tabia’i?

Amsa: Ta fuskar ka’idoji na ilimi, aikin ma’asumi yana nuni a kan halascin abu, amma barinsa a kan aikata wani abu ba ya nuni a kan haramcin abu. Idan muka dauka cewa sahabbai ba su yin sabo ko kuskure, wato muka yi musu hukuncin ma’asumai, a nan rashin aikatawarsu ba ya zamar mana dalili a kan haramcin abu ba. Bayan haka, ma’auni a wajen sanin haramci ko halascin abu shi ne maganar Manzo ko magadansa ma’asumai (a.s) don haka muna iya ganin wannan nau’i na Tawassuli a fili a cikin ruwayoyin Manzo da addu’o’in Ahlul baiti (a.s)

Kalu balanta ta biyu: Halittu ba su da hakki a kan Allah:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next