Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



Wannan addu’a kuwa tana nufin cewa ya Allah idan harm u ba mu cancanci ka yi ruwa saboda mu ba, to albarkacin ammin Manzo domin alakar da suke da ita a tsakaninsu ka aiko mana da ruwan sama.

Saboda haka idan a nan ana nufin kamun kafa da wani mutum ne, to kamun kafa da Manzo ya fi komai dacewa, domin kuwa Abbas ya samu darajarsa ne daga Manzo (s.a.w) saboda haka me ya sa a nan ya bar Manzo ya yi kamun kafa da Abbas, wannan shi ne abin tambaya a nan?

Amsar wannan kuwa shi ne a wajen rokon ruwa ana kamun kafa ne da wadanda masu rokon ruwa suke daya da shi wajen bukatr ruwan, kamar kananan yara da tsofaffi, ta yadda zasu motsa rahamar Ubangiji, su ce ya Allah idan mu ba mu cancanci wannan ba to wadannan kananan yara da tsofi sun cancanta ka aiko saboda su.

Saboda haka wannan ya cancanta ga ammin Manzo wanda ya kasance yana raye a wannan lokaci, ba wai Manzo ba domin kuwa shi a wannan lokaci ya bar duniya kuma halin da suke ciki ya bambanta.

Wadanda suke sabani a kan halascin kamun kafa ko tawassuli da manyan bayin Allah suna fito-na-fito ne da wannan hadisi, saboda haka ko ta halin kaka suna kokari ne suga sun karkatar da ma’anarsa, suna cewa abin da khalifa yake nufi a nan yana kamun kafa ne da addu’ar Abbas, ba wai yana kamun kafa ba ne da shi kansa Abbas ko wani matsayi na shi. Wannan tawili kuwa ta fuskoki daban-daban ba zai inganta ba:

Na farko: Sallar rokon ruwa da addu’ar, umar ne ya gabatar da su ba Abbas ba, saboda haka a nan babu magana a kan addu’ar Abbas.

Abin da kuwa yake tabbatar mana da cewa wannan addu’a umar ne ya yi ta ba Abbas ba, lafazin da ya zo a cikin addu’ar kamar haka: Ya Allah mun kasance muna kamun kafa da Manzo ka shayar da mu, yanzu muna kamun kafa da ammin Manzo ka shayar da mu, a wannan lokaci sai ruwa ya sauka aka shayar da su.

Saboda haka wannan yana nuna cewa wanda ya gabatar da wannan shiri tun daga farko har karshe khalifa ne, ba wai Abbas ammin Manzo ba, ballantana Umar ya yi kamun kafa da addu’arsa.

Na biyu: Dalili na biyu shi ne a cikin babin da wannan addu’a ta zo yana magana ne a kan neman mutane daga shigaba don ya roka musu ruwan sama yayin da aka samu fari da rashin ruwan sama.

Wannan yana nuna cewa mutane su ne suka nemi khalifa da ya roka musu ruwan sama, shi kuma ya amsa musu rokn da suka yi masa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next