Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



 

3-Sabani Tsakanin Mabiya Ibn Taimiyya Da Sauran Musulmi

An rubuta wasu litattafai daga bangaren masu inkarin tawassuli da bayin Allah daga bayan-bayan nan, inda suke nuna cewa wani sabani ne tsakanin Shi’a da Sunna, alhalin kuwa wannan sabani bai shafi tsakanin Sunna da Shi’a ba, wani sabani ne wanda yake tsakanin mabiya Ibn Taimiyya da sauran al’ummar musulmi, kuma a baya kadan mun kawo wasu Littattafan manyan malaman AhlusSunna wadanda aka rubuta a kan raddi ga Ibn Taimiyya da mabiyinsa Muhammad Bn Abdul wahab, don haka muna iya gane cewa sabani ya fari ne tsakanin wadannan mutum biyu da mabiyansu da sauran dukkan al’ummar musulmi wadanda suka tafi a kan ingancin kamun kafa da waliyyan Allah, wato sauran musulmi ba su da sabani a kan haka, don haka ba sabani ne ba tsakanin Shi’a da Sunna kamar yadda wasu suke riyawa, kamar yadda muka gani da kuma abin da zamu gani a nan gaba wanda yake tabbatar da hakan.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012

 



[1] Fathul bari:2/492Siratu halabi:1/116

[2] -Kitabul Um na Shafi’i:1/23.

[3] -Sahihul bukhari:2/32 babin istiska.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next