Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



Sannan a cikin hadisai da dama zamu iya ganin irin wadannan hakkoki. Don haka a nan kawai zamukawo daya daga cikin a matsayin misali kamar haka: Manzo (s.a.w) yana cewa ya wajaba ga Allah ya taimaki wanda ya yi aure domin tsoron kada ya fada a cikin haram.

Kalu bale na uku: Wannan nau’in na kamun kafa ko Tawassuli kiran wanin Allah ne. Ayoyi da yawa a cikin Kur’ani mai girma sun yi bayani a kan cewa musulmi bai halatta ba ya kira ko ya roki wanin Allah, kamar yadda Allah madaukaki yake cewa: “Kada ku kira wani tare da Allah”[13]. “Lallai wadanda kuka kira suma bayi ne kamar ku”[14].

Daga wadannan ayoyi guda biyu muna fahimtar cewa a wajen addu’a babu wanda ya kamata a kira sai Allah madaukaki shi kadai ba wanin Allah ba, don haka kamun kafa da wani ko matsayin wani kiran wanin Allah ne.

Amsa: Abin da yake mafi rashin tushen a cikin kalu balantar da ake yi dangane da kamun kafa ko Tawassuli shi ne wannan wanda aka ambata a sama, wanda kuma da wannan ne masu kin amincewa da tawassuli suke riko da shi, ta yaddacikin rashin adalci suke dora ayoyin da suka zo a kan mushrikai masu bautar gumaka a kan musulmai da manyan bayin Allah. Duk da cewa wadannan ayoyi sun sauka ne a kan mushrikai wadanda suke daukar gumakansu matsayin alloli komasu tafiyar da duniya. Ba kamar yadda musulmi ba ya dauka cewa Manzo (s.a.w) bawan Allah ne kuma mai kira zuwa ga kadaita Allah madaukaki, sakamon ana yin amfani da irin wadannan ayoyi a wajen irin haka, don haka zamu yi dan bayani a kan wadannan ayoyi kamar haka:

1-Ayoyin da suke cewa: Kada ku kira wanin Allah, wadannan ayoyi suna nufin kiran Allah da ma’anar bauta ne, ba wai da nufin kira ba kawai ga wani mutum mai matsayi koda kuwa da niyyar cewa shi kawai wani mutum ne mai tsarki, domin kuwa a matsayin sheda a ayar da ta gabata yana cewa: “Kada ku kira wani tare da Allah”. Idan cikin wannan aya ana nufin kira ko roko ne kawai ba yana nufin bauta ba ne, to zai zamana ma’anar wannan aya ta sabawa umurnin Kur’ani, domin kuwa Kur’ani yana ba da umarni ga musulmi cewa su tafi wajen Manzo su neme shi da ya roka musu Allah gafara, sannan shi ma ya gafarta musu.[15]

A nan mutum yana kiran Ubangiji yayin da yake neman gafarar Allah da kansa, sannan yana kiranmanzo yayin da yake so ya gafarta masa. Saboda haka ma’nar cewa kada ku kira wani tare da Allah shi ne, kada ku hada wani atre da Allah wajen bauta.

Kamar haka ne a cikin aya ta biyu ma babu bambanci, domin kuwa abin da ake nufi da “kuke kira” a cikin aya ta biyu ana nufin bauta ne, domin kuwa jimalar da ta zo a bayanta wacce kuma take haramta yin hakan tana cewa: “Domin kuwa su bayi ne kamarku”. Wato kada ku bautawa wadannan gumakan na karya domin kuwa ba su da wani bambanci da ku, suma kamarku suke bayine na Allah.

Saboda haka hanin da aka yi na kada a kira wani tare da Allah ko kuma a kira shi ba tare da Allah ba, ana nufin kira ne wanda yake da ma’anar bauta, wanda ya samo asali ne daga imanin mutum da cewa shi wannan abin a matsayin Allah ne, ba wai kawai kira ba tare da wannan imanin ba, domin kuwa rayuwar dan Adam baki daya ta doru a kan haka ne. Kur’ani mai girma yana cewa: “Zamu kirawo ‘ya’yammu kuma ku kirawo ‘ya’yanku”[16].

Sannan a cikin wata aya ana cewa bai kamata ku kira Manzo ba kamar yadda kuke kiran sauran mutane a tsakaninku, ga abin da ayar take cewa: “Kada ku sanya kiran Manzo kamar a tsakaninku kamar yadda kuke kiran junanku”[17].

Saboda haka kiran da ake magana a cikin wannan aya ba ana nufin kawai kira ba haka nan, ana nufin kira da sunan bauta ga Allah ko ga wani wanda mutum ya dauka cewa shi ne yake tafiyar da wasu ayyukan Ubangiji.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next