Mutum Mai Kamala



Khadiza (A.S) ta auri Manzo (S.A.W) tana budurwa a lokacin ba ta taba aure ba, tana ‘yar shekara goma sha takwas, shi kuma yana dan shekara ishirin da biyar.

Abu Talib (A.S) ya tafi wajan amminta Amru Dan Asad ya nemi aurenta ga manzo (S.A.W), domin an kashe babanta kafin wannan lokacin.

Abu Talib (A.S) yana cewa a yayin da ya tafi neman aurenta ga Manzo (S.A.W): “Godiya ta tabbata ga ubangijin wannan daki (na ka’aba), wannan da ya sanya mu daga tsatson Ibrahim (A.S) da kuma zuriyar Isma’il (A.S)… sannan dan dan’uwana… -yana nufin manzon Allah- ba a auna shi da wani mutum daga kuraishawa a sikeli daya sai ya yi rinjaye, kuma ba a kwatanta shi da wani mutum sai ya fi shi daukaka, … ga shi yana son Khadiza (A.S), mun zo muna neman aurenta a wajanka, da yardarta da kuma umarninta, kuma sadakin yana kaina a dukiyata da zaku nema hannu-da-hannu ko kuma ajalan –na rantse da ubangijin wannan Dakin na Ka’aba- (wannan aure) rabo ne mai girma, addini mai yaduwa, kuma ra’ayi cikakke”.

Sai Muhammad (S.A.W) ya tashi domin ya tafi tare da Abu Talib (A.S) gida, sai Khadiza (A.S) ta ce da shi: ina zaka tafi, ai gidana gidanka ne kuma ni mai hidimarka ce.

Haka nan ne ya aure ta (A.S) aka kafa gida mai haske cike da shiriya. Manzo (S.A.W) yana fadi game da ita: Khadiza (A.S) ta yi imani da ni yayin da mutane suka kafirta da ni, ta gaskata ni yayin da mutane suka karyata ni, ta taimake ni da dukiyarta yayin da mutane suka hana ni, kuma Allah ya arzuta ni ‘ya’ya da ita ya hana ni ‘ya’yan mutane (ta wata matar)[6].


Albishir Da Zuwan Manzo (S.A.W)

Hakika an samu albishir da zuwan manzo (S.A.W) tun kafin zuwansa da shekaru masu yawa kamar yadda yake a sunnar Allah ta yin albishir da wani babban abu ga mutane tun kafin zuwansa.

Daga cikin inda aka samu albishir da zuwan manzo (S.A.W) akwai:

1.     Injil; Yohana:

“Idan kun kasance kuna so na to ku kiyaye wasiyyata, ni zan nema daga Uba sai ya ba ku wani abin yabo (Ahmad), domin ya zauna tare da ku har abada[7].

A cikin wannan fakara ya ci gaba da cewa: “Ba zan yi muku magana da yawa ba; domin shugaban wannan duniya yana tafe”. Kuma ya ce: “Amma abin godewa ruhi mai tsarki da baban zai aiko shi da sunana, shi ne zai sanar da ku komai, kuma zai tunatar da ku dukkan abin da na gaya muku”. Da sauran abubuwan da suka zo game da hakan. Idan mun lura zamu ga cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next