Mutum Mai Kamala



A.   Marhalar boyewa

B.    Marhalar bayyanarwa ga dangi

C.   Marhalar bayyanarwa ga mutane


Kiran Mutane A Bayyane

Ruwayoyi da dama game da yadda ya bayyanar da da’awarsa ga mutane suna da yawa, amma zamu kawo daya daga ciki ne, an rawaito cewa: manzo (S.A.W) ya tsaya a kan Safa, sanna sai ya kira kuraishawa; sai suka taru, sannan sai ya ce da su: “Shin da zan ba ku labari cewa wasu mahaya sun kawo muku hari ta kan wannan dutsen zaku gasgata ni?. Suka ce: Na’am, kai a wajanmu ba abin tuhuma ba ne, kuma ba mu taba jin karya daga gareka ba. Sai ya ce: To ni mai gargadi gareku (daga wajan Allah) daga azaba mai tsanani. Sai Abu lahab ya mike tsaye ya ce da shi: Kaiconka! Yanzu saboda wannan ka tara mutane?. Sai mutane suka watse, sai Allah ya saukar da: Surar lahab.

Kuraishawa sun dauki matakin farko domin tsayar da wanna da’awa ta manzo (S.A.W) da tayin abubuwa gun Abu Talib (A.S) a kan cewa sharadin shi ne manzo (S.A.W) ya tsayar da kiransa kuma ya janye maganarsa, wadannan abubuwa suna hada da:

·        Ba shi dukiya mai yawa

·        Ba shi mulki a tsakaninsu

·        Ba shi mata kyawawa da yake so

Sai Abu Talib (A.S) ya tambayi manzo (S.A.W) domin ya ji menene zai fada, amma sai manzo ya ba shi amsa cewa; Da zasu dora rana a hannunsa na dama, wata a na hagu da ba zai bari ba, don haka ne ma Abu Talib (A.S) ya ce masa: Ka tafi ya dan dan’uwana ka ci gaba da abin da kake so, wallahi ba zan mika ka a kan wani abu ba har abada[11].

Da kuraishawa suka ga wannan ba ta ba su abin da suke so ba sai suka koma da jifa da kalmomi da isgili da tuhumomi masu yawa kan annabi (S.A.W) da kiransa da abubuwa mabanbanta kamar:

1.     Jifansa da hauka
2.     Jifansa da sihiri
3.     Sanya kaya a kofar gidansa
4.     Wulakanta shi
5.     Azabtar da wadanda suke yin imani da shi
 

Da manzo ya ga yawancin masu musulunta ba su da kariya kamar yadda yake da ita daga Abu Talib (A.S) sai ya umarce su da yin hijira zuwa Habasha, yana mai gaya musu: “A Habasha akwai wani sarki da ba a zaluntar wani gunsa”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next