Mutum Mai Kamala



4-        Fasadi da lalacewar dabi’a, kamar yaduwar caca, da giya, da zina, da luwadi, da karuwanci.

5-        Binne ‘ya’ya mata, wannan wata al’adace mai muni da kur’ani ya yi magana game da ita a matsayin laifi mai muni da ba zai bari haka nan ba a lahira ba tare da ya yi hisabi a kai ba.

Ya ce: “Idan aka yi wa dayansu albishir da mace sai fuskarsa ta zama baka yana mai bakin ciki, yana boye kansa daga mutane daga munin aibin da aka yi masa albishir da shi, shin zai rike shi ne a wulakance ko kuma ya turbude shi a turbaya, hakika abin da suke hukumtawa ya munana”. Nahal: 58-59.

Ya ce: “Idan wacce aka binne ta aka tambaye ta. Da wane laifi ne aka kashe ta”. Takwir: 8-9.

Saboda haka ne mace ta zama an haramta mata dukkan hakkokin zamantakewar al’umma har da gado, namiji ya zama yana auren matar babansa idan ya sake ta ko bayan wafatinsa, da yawa daga ‘ya’ya suka yi fasin-fasin da matar babansu daya bayan daya, kamar yadda namiji yake gadon matar dan’uwansa idan ya mutu ya bar ta tamkar yadda yake gadon kayan gida, hada da cewa su ba sa ba wa ‘ya’ya mata gado kamar yadda suke ba wa ‘ya’ya maza.

6-        Shan jini, da cin mushe, da cin naman alade, da cin naman sauran dabbobi da suke kashewa ta hanyar rashin tausayi.

7-        Cin riba, wannan kuma yana zaman kashin bayan cinikayya a tattalin arzikinsu.

8-        Kwace da karfi, kwace abin da yake hannun mutane da kai hari, da kisa, da kashewa, yana daga al’adu masu karfi a wajansu, har ma ya zama yana daga abubuwan alfahari gun maza.

9-        Amma a janibin ilimi da wayewa, mutanen hijaz sun siffantu da rashin iya rubutu da karatu, wadanda suka san karatu da rubutu a Makka gaba dayanta adadinsu bai wuce mutane goma sha bakwai ba daga kuraishawa kafin zuwan musulunci.

10-   Daga cikin munanan al’adunsu a wancan zamani akwai abin da Ja’afar Dan Abi Talib (A.S) ya fada yayin da ya yi huduba a gaban Najashi sarkin Habasha yana mai cewa: “Ya kai sarki! Mu mun kasane mutane ne na jahiliyya, muna bauta wa gumaka, muna cin mushe, muna zo wa alfasha, muna yanke zumunci, muna munana wa makwabci, mai karfi a cikinmu yana cin mai rauni, mun kasance a haka…”[3]. Wannan ita ce hakikar larabawa kafin musulunci.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next