Mutum Mai Kamala



17. Dukkaninmu daga Adam (A.S) muke shi kuma daga kasa

18. Wanda ya fi a wajan Allah shi ne wanda ya fi tsoron Allah

19. Babu kabilanci a musulunci, babu bambanci tsakanin balarabe da waninsa ko fari da baki

20. Wanda yake nan ya isar wa wanda ba ya nan

21. Bayanin hukuncin gado da masu gado

22. Bayanin hukuncin jayayya game da yaro

23. Haramcin da’awar ubantakar wani mutum daban

Mai karatu yaya kake gani da dukkan duniya zata kiyaye irin wadannan dokoki da dubunnansu wadanda musulunci mai girma ya zo da su ga dan Adam domin kai shi zuwa ga kamala mafi daukaka.

Ayyana Halifa

Kamar yadda muka sani cewa; duk wani mai hankali ba zai yiwu ya tafi ya bar gidansa ba, ba tare da mai kula da gidan ba, kodai matarsa ko wani makamancin hakan, kamar yadda hankali yana hukunci da wautar mutumin da yake tafiya ya bar al’ummar da yake shugabanta kara zube ba tare da ya ayyana mata mai kula da ita.

 Idan haka al’amarin yake ba yadda za a yi Manzon rahama mai tausayi ga al’umma wanda ya bayyana mata hatta da hukuncin shiga ban daki da yadda ake fita ya zamanto ya bar wannan al’amari mai girma na tafiyar da al’amuran musulmi ba tare da ya ayyana mai kula da shi ba, alhalin ya san irin al’ummar da ya bari wacce take cike da munafukai da masu son ganin musulunci ya rushe, kuma ga kafiran duniya na daulolin farisa da rumawa sun fara kawo wa daula hari, hada da cewa akwai jahiltar hukunce-hukuncen addini da musulmi kansu suke bukatar wanda zasu cigaba da komawa zuwa gareshi domin dauke kishirwar tambayoyinsu da abubuwa masu yawa da ba sa kirguwa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next