Mutum Mai Kamala



San Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Allah mai girma a kan kammala addini da cikar ni’ima da yardar ubangiji da manzancina da shugabanci ga Ali (A.S) bayana”.

Sannan sai ya yi umarni aka kafa hema ga Ali (A.S) kuma musulmi su shiga wajansa jama’a-jama’a suna yi masa sallama da bai’a a kan shugabancin muminai, sai duk mutane suka yi hakan, ya umumarci matansa da sauran matan muminai da suke tare da shi su ma suka yi bai’a.

Daga cikin na gaba wajan yi masa murna da bai’a akwai Abubakar da Umar dan Khaddabi, kowannensu yana cewa: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abu Talib, ka wayi gari, ka yi yammaci shugabana kuma shugaban dukkan mumini da mumina[13].


Karshen Rayuwar Manzo Da Wafatinsa

Manzon Allah ya kasance babu wani abu da yake raba shi da Ali a karshen rayuwarsa, yana mai yi masa wasiyya da karfafa shi kuma da shirya shi domin daukar nauyi mai girma da zai hau kansa, ya kasnce mai lizimtar dakin Imam Ali (A.S), kuma ya kasnce yana dafa shi domin tafiya yayin da rashin lafiyarsa ya tsananta har ya yi wafati a hannunsa kuma dakin wasiyyinsa imam Ali (A.S) kamar yadda imam Ali ya fada a daya daga hudubobinsa[14].

Ba wanda yake tare da Manzon Allah a lokacin wafatinsa sai imam Ali (A.S) da ‘yarsa (A.S) da wasu daga Banu Hashim da iyalansa. Yayin da mutane suka samu labarin wafatinsa Madina gaba dayanta ta hau kuka da bakin ciki mai tsanani, Umar dan Khaddabi ya daga takobi ya hana mutane cewa Manzo ya rasu har sai da Abubakar ya zo. Sannan Abubakar da Umar dan Khaddabi da wasu daga abokansu suka gaggauta zuwa Kangon Banu Sa’ida (Sakifa) suka tarar da wani taro na Ansar a can da suke neman zabar halifa daga cikinsu, wannan al’amarin ya kai ga jayayya mai tsanani da kuma ganganta manta bai’ar da aka yi wa Ali (A.S).

A daya bangaren imam Ali da Ahlin gidansa sun shagaltu da shirya Manzo (S.A.W) da bizne shi, Ali ya wanke shi ba tare da ya cire rigarsa ba, Abbas da dansa Fadl suka taimaka masa da zuba ruwa, ya kasance yana cewa: Ina fansar ranka da babana da babata, kanshinka ya girmama kana rayayye da kana fakakke[15].

 Sannan imam Ali (A.S) ya dora Manzo akan wani gado ya yi masa salla kuma ya umarci musulmi da su shiga su yi masa salla ba tare da jam’i ba, suna shiga jama’a-jama’a suna yi masa salla, imam Ali (A.S) ya kasance yana cewa: “Aminci ya tabbata gareka ya kai wannan annabi da rahamar Allah da albarkarsa. Ya ubangiji mu muna shaidawa cewa hakika ya isar da sakon da ka saukar masa, ya yi nasiha ga al’umma, ya yi jihadi a tafarkin Allah, har Allah ya daukaka addininsa, ya cika kalmarsa, ya ubangiji ka sanya mu cikin masu bin abin da ka saukar gareshi, ka tabbatar da mu bayansa, ka hada tsakaninmu da shi. Sai mutane su ce: Amin. Har maza da mata da yara suka yi salla gareshi, tsira da amincin Allah su tabbata gareshi da alayensa.

Ya binne Manzo a dakin da ya yi wafati, ya sanya shi cikin kabari, ya yaye fuskarsa, kuma ya daidaita kumatunsa mai tsarki a kan turbaya, sannan sai ya zuba kasa. Amma musulmin da suke a Sakifa domin nada halifa bisa jayayya mai tsanani babu wani daga cikinsu da ya samu damar zuwa wajan janazar Manzo ko yi masa salla ko bizne shi. Aminci ya tabbata gareka ya Manzon Allah! ranar da aka haife ka, da ranar da ka yi wafati, da ranar da za a tashe ka rayayye.

Daga Kyawawan Dabi’un Annabi

Allah madauki yana cewa: “Saboda (kai) rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a garesu, kuma da ka kasance mai kaushi mai kaurin zuciya da sun watse daga gefenka”[16].

Haika Manzon rahama (S.A.W) ya kasance mai kyawawan dabi’u marasa misali, don haka duk abin da alkalami yake rubutawa to ya gaza ya kawo hakikaninsu, amma zamu yi nuni da wasu kadan daga ciki.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next