Mutum Mai Kamala



Ya kasance mai kaskantar da kai, kuma rayuwarsa madaidaiciya ce, ta yadda idan bako daga larabawan kauye ya zo mazauninsa yakan tambaya wanene Muhammad a cikinku[17]?. Duniya ba ta rude shi ba, ya kasance yana kallonta da idanun takawa da tsentseni, kuma bai fada a tarkonta ba[18]. Ya kasance ba ya yaudara, yana cika alkawuransa, yana sadar da zumuncinsa, ba ya bayar da dama ga wani ya yi magana a kan wani, domin yana son ya bar mutane yana mai kubutacciya zuciya; wato ba ya kallonsu da wani abu[19].

 Ya kasance misali ne a yalwar kirji da hakuri da rangwame. Anas yana cewa: Manzo (S.A.W) ya kasance yana da wani abin sha na sahur, kuma da na shan ruwa da yamma, wani lokaci guda daya ne ma, wani lokaci madara ce, wani lokaci kuma gurasa ce da ake taunawa a tsotse, wata rana na yi tanadinta, sai ya jima bai dawo ba, sai na yi tsammanin ya sha ruwa a wajan wani daga sahabbansa ne, sai na shanye, sai ya zo bayan sallar isha da awa daya, sai na tambayi wadanda suke tare da shi cewa; shin Manzo ya sha ruwa a wani waje ko kuma wani ya gayyace shi? Sai suka ce: A’a. Ya ce: Sai ya kwana ya wayi gari da azumi bai ci komai ba, kuma bai tambaye ni ba, bai kuma taba maganarta ba har yau[20].

Ya kasance yana son salla da yawa, idan mutane suka zo sai ya dakatar da salla ya saurare su, idan suka tafi sai ya cigaba.

Yana girmama kowa, kuma ma’aunin daraja a wajansa shi ne imani da aiki… ba ya ganin kima don dukiya do matsayi ko alfarma, ya kasance mai tausayi ga abokin tafiyarsa mai himmantuwa da sha’aninsu da bukatunsu[21].

Rangwamensa Da Afuwarsa

Baya daga cikin dabi’ar Manzo (S.A.W) daukar fansa a kan wanda ya munana masa, yana mai rangwame ne ga masu keta iyakarsa, kuma yana fuskantar munanawarsu da hakuri da juriya da afuwa da rangwame. Duk da irin wahala da cutarwa da ya fuskanta daga Kuraishawa a farkon kiransa amma bayan Fathu Makka sai ya yafe musu gaba daya. Kamar yadda ya yafewa Wahashi makashin amminsa Hamza da kuma Abu Sufyan da matarsa Hindu.

Duk da haka bai taba yarda da ketare iyakar Allah ba, kuma ba ya jin tsoron zargin mai zargi game da addinin Allah, shi ya sa ma yayin da Almakhzumiyya ta yi sata bai karbi shiga tsakiyar Usama dan Zaid ba, yana cewa[22]: Abin da ya halakar da wadanda suke gabaninku shi ne sun kasance idan mai girma ya yi sata a cikinsu sai su bar shi, idan mai rauni ya yi sata sai su tsayar da haddi a kansa.

Tsarkinsa Da Tsaftarsa

Ya kasance yana kiyaye jikinsa da tufafinsa a kan tsafta kodayaushe, yana amfani da mafi kyawun turare, imam sadik (A.S) yana cewa: “Yana kashe kudi a kan turare fiye da yadda yake kashewa a kan abinci”[23]. Duk inda ya wuce kanshin turare yana tashi, ya kasance yana kallon mudubi yana taje gashinsa, wani lokacin yana kallon ruwa ne ya gyara gashinsa, ya kasance yana ado ga sahabbansa ballanta matansa. Yana cewa: “Allah yana son idan bawansa zai fita wajan ‘yan’uwansa ya yi shiri ya yi ado”[24].

Ibadarsa Da Zuhudunsa

Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai yawan shagaltuwa da salla, an rawaito daga Abu Abdullah (A.S) yana cewa: Ya kasance idan Manzon Allah ya yi sallar isha sai ya yi umarni da a kawo masa ruwan alwala da asuwakinsa, a ajiye turba a gun kansa, sai ya yi bacci kadan sannan sai ya tashi ya yi asuwaki ya yi alawala ya yi salla raka’a hudu, sannan sai ya yi bacci kadan sai ya tashi ya yi asuwaki ya yi alwala ya yi salla, yana asuwaki duk sadda ya tashi daga baccinsa[25].

Ya kasance yana tsawaita kaskantar da kai ga Allah da tsayuwa gabansa har sai da kafafunsa suka kumbura[26]. Ya kasance mai yawan tunani game da abin da yake gewaye da shi na halittar sama da kasa da rana da makamancinsu, saudayawa yakan yi tunani game da girman mahalicci. Amma game da zuhudunsa ya isa girman zuhudunsa cewa kyale-kyalin duniya ba su taba fitinarsa ba, kuma ba su taba jan hankalinsa ba.


[1] Surar Kalami: 3 – 4.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next