Zabar Mace Ko Namijin Aure



5- Kiyaye adalci tsakanin mata: Nisa’I: 3.

6- Namiji da mace daidai suke a kamalarsu ta ‘yan adamtaka: Nahal: 97.

7- Kiyaye hakkokin mata: Nisa’I: 7.

8- Abin da namiji zai yi wa mace mai kin shimfidarsa; Na farko: Wa’azi. Sannan sai: kauracewa shimfidarta. Sannan sai: sanya karfi da duka da takurawa daidai yadda shari’a ta gindaya. Nisa’I: 34. 

9- Kyautata wa mace yayin da ake ci gaba da zaman tare ko yayin da za a rabu: Bakara: 231.

10- Bayar da kyauta mai dacewa ga mace yayin da za a rabu: Ahzab: 49.

11- Bayar da kyauta ga mace daidai ikonsa idan za a rabu kuma ba a san juna ba a shimfida, kuma ba a ayyana sadaki ba: Bakara: 236.

12- Bayar da rabin sadaki ga mace yayin rabuwa kuma an ayyana sadaki amma har suka rabu din ba su san juna ba a shimfida: Bakara: 237.

13- Kada a takura wa mace domin ta halatta masa sadakinta: Nisa’I: 19.

14- Dokokin hakkokin mace bayan rabuwa, kamar wajan zamanta, da rashin kuntata mata, da ciyar da ita: dalak: 6.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next