Zabar Mace Ko Namijin Aure



*Wani lokaci matar mutum ta kan cutar da shi wajan ta taimaka masa ko makamancin haka, wannan wani abin yafewa ne da kauda kai saboda yana faruwa ne daga kauna da son taimakawa daga mata.

Nasihohin Wata MataGa ’Yarta

 Wata mata yayin tarewar ’yarta gidan miji ta yi mata nasiha ne kamar haka tana mai cewa da ita:

**Ki zama baiwarsa zai zama bawanki [wannan magana tana da hikima sosai domin duk wanda kake jin dadinsa to shi kake kyautatawa]

**Ki kaskantar da kai gareshi.

**Ki ji ki bi.

**Ki bi idanunsa [wato ki duba duk abin da yake kayatar da shi ki yi abin da ba ya so ko yake kinsa to ki bari]

**Ki kuma bi hancinsa [wato abin da yake so na kanshi ki yi wanda ba ya so ya ji na daga wari ki nisance shi]

**Ki bi lokacin baccinsa [wato ki kula a lokacin bacci kada ki nisanci wajan baccinsa, wato shimfidarku daya, zaninku daya, kuma ki yi masa tabarruji]

**Ki bi abincinsa da abin shansa [wato kada lokacin cin abinci ya yi ya nema ya rasa ko ba ki dafa masa ba]

**Ki kiyaye masa dukiyarsa da kula da ’ya’yansa da tarbiyyarsu, da iyalansa, da uwayansa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next