Zabar Mace Ko Namijin Aure



Shimfida

A musulunci an yi umarni ne da a yi aure ba domin biyan bukata ta duniya ko ta sha’awa ba kawai, akwai bukata ta gina al’umma saliha da zata ci gaba da daukar nauyin isar da sakon Allah a duk fadin Duniya, wanda wannan yana bukatar taimakekeniya tsakanin ma’aurata, sa’annan akwai samun nutsuwa ta ruhi da dan Adam yana bukatarsa wanda an sanya shi ne ya zamanto ta hanyar zamantakewa tsakanin miji da mata.

Misali mace koda ta yi ilimi kuma ta samu komai na wannan duniya, da dukkan ni’ima, haka nan ma namiji, idan ba su da mai debe musu kewa ta fuskacin zaman auratayya to akwai wani gibi babba da ba su cike shi ba, wanda ba ya samuwa sai ta hanyar auratayya, wacce kur’ani mai girma ya yi nuni da ita[2], kamar yadda a zamantakewar tare tsakanin ma’aurata idan aka mayar da kauna da so suka koma kiyayya da gaba, abin yakan fi zama ba tare da mai debe kewa ba muni. Kamar yadda haka nan ana son yin aure da wuri ga wanda ya balaga matukar ya samu yalwa, domin a cikin rashin yin hakan akwai fitina a bayan kasa da fasadi mai girma kamar yadda ya zo daga Ahlul Baiti (A.S)[3]. Mu sani akwai kamalar da ba ta yiwuwa a san ta ko a kai zuwa gareta sai ta hanyar aure, kuma ba ta samuwa ta hanyar zaman banza da fasikanci. Irin wadannan abubuwan sun hada da: sanin ma’anar ciyarwa, yafewa, soyayya, hakuri, juriya, daukar nauyin mutane, reno, tarbiyyar ‘ya’ya, fahimtar kimar iyaye, tunanin gida da sauransu.

Ayatul-Lahi makarim shirazi yana cewa: saudayawa daga cikin abubuwa kamar ma’anar soyayya, da kauna, da yafewa, da kyauta, da baiwa da tausayi, da fansar rai, ma’anarsu ba ta ganuwa da fahimtuwa sai da aure, wanda zaman banza ba tare da aure ba da matar haram ko zaman gwauranci da rashin aure ba za a iya fahimtar hakikaninsu ba, kuma riskarsu tana yiwuwa ta hanyar zamantakewar aure ne kawai[4].

Abubuwan Da Sukan Jawo Rashin Aure Da Wuri

Masu ilimi sun kawo wasu abubuwa kamar haka da sukan kawo jinkirin aure:

1- Tsawon muddar lokacin karatu: ta yadda saurayi ko budurwa kafin ya kai ga kammala jami’a ya kai shekara talatin zuwa talatin da biyar a mafi yawan lokuta, saudayawa wannan yakan jefa wasu cikin halin da suka katse karatu idan ba zasu iya hada biyun ba, don haka yana kan al’umma da gwamnatocinsu su yi tunanin maganin wannan koda ta hanyar tallafi ne a kan ‘yan makaranta. Misali a nan a kasar farisa sukan yi kokarin yi wa dubunnan daliban jami’a aure a kyauta kowace shekara da kuma ba su tallafi.

2- Samun damar yin alakar haram: Yawaitar gidajen karuwai da wajajen fasikanci saudayawa yakan sanya wasu samari su ga ya fi musu sauki su je su yi mummunar mu’amala ta haram da matan banza na wani dan lokaci tsawon rayuwar samartakarsu. Wannan ma wani abu ne da musulunci ya sanya mafita gareshi ta hanyoyi da dama kamar haka:

a- Tallafin aure da wuri daga baitul mali ga dukkan wanda ba zai iya aure ba kuma da bukatar hakan domin ya balaga.

b- Tarbiyyantarwa ta hannun malamai, da kafafen watsa labaru da jaridu da makarantu.

c- Hana gidajen fasadi da kulle duk wani waje da ake ashararanci.

d- Wayar da kan mutane a ilmance domin su san illar wannan mummunan hali da abin da yake jawowa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next