Zabar Mace Ko Namijin Aure



*In za a hadu a hadu kamar yadda Allah ya ce, haka ma rabuwa, saboda haka wajan rabuwa sai da shedu da cikar sauran sharudda kamar yadda suke a Addini.

*Kada a fara neman aure sai in da gaske ana so a yi auren ne.

*Babu laifi mace ta nemi namiji ya aure ta, wannan ba aibi ba ne ga mace, saboda haka mace in ta ga tana son wani tana iya shaida masa domin tarihin salihan bayi ya nuna mana haka.

*Wajan yin zance tsakanin saurayi da budurwa dole ne su kiyaye dokokin Allah kamar haramcin ganin abin da yake ganinsa haramun ne.

*Kada mai neman aure ya sanya sharudda masu wahalar cika ga wacce yake son aura wadannan saudayawa ba su sami burinsu ya cika ba.

*Kada a yi yaudara yayin neman aure haka ma a kula da kyawawan dabi’u.

*Kyautatawa mace haka nan ita ma ta kyautata masa, kuma a rika godiya kan abin da ake yi wa juna na alheri, wannan kan sanya kowane bangare ya dada himma kan abin da yake yi na alheri.

*Kar ka ce ai ba wajibi ba ne in yi mata kaza, domin kai ma akwai abubuwa da yawa da ba wajibi ba ne a kanta, kuma tana yinsu.

*Ku raba ayyukan kwanaki da suke hawan kanku a matsayinku na masu auratayya.

*Kada mace ta yi wa miji gorin satifiket ko wata shaida ta ilimi ko wani abin da ka iya nuna gori a kansa haka nan shi ma haka.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next