Zabar Mace Ko Namijin Aure



3- Ya taimakawa kansa da yin azumi domin dawo da karfin iradarsa.

4- Ya shagaltu da mudali’ar littattafai, da nau’o’in irin wasanni kamar wasan gudu da tseran doki da sauransu.

5- Iyaye su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu tun farkon rayuwarsa, ta yanda zasu kula da dukkan halayensa domin gyara da ba shi tarbiyya ta gari.

6- Dole ne al’umma da hukuma su bayar da muhimmanci na musamman kan sha’anin aure.

7- Mai wannan halin ya duba irin bala’in da yake fada masa na cututtukan ruhi da na jiki, kamar cututtukan fata, rashin jin cikakken dadin kusantar mace, rashin matsayi a al’umma saboda matsalar jijiyoyi da gajiyawar jiki, da sauransu[10].

Mu sani yawan duba littattafan hikima da na ilimi[11], da yawan tafiye-tafiye[12], da wasannin motsa jiki[13], da koyon harbe-harbe, da koyon sukuwar doki, da iyo a ruwa, suna daga cikin abubuwan da suke karfafa ruhin mutum[14], kuma suna kawo lafiyar jiki da ta ruhi da nishadi ga rayuwar mutum, kamar yadda suna kawo farin ciki da annashuwa.

Sha’awar Da Ta Fita Daga Al’ada

Daga cikin shawarwari da aka bayar ga mai yawan sha’awar da ta fita daga al’ada, musamman wadanda sha’awarsu ta kai su ga lalacewa da babu wani haramun da ba zasu iya bari ba ta hanyar biyan bukatarsu ta haram, sun hada da:

1- Tunawa da munin wannan hali, da abin da yake haifarwa na cututtukan ruhi da jiki, da jawo wa mai wannan hali saurin tsufa da mutuwa a rayuwarsa ta duniya.

2- Karya karfin sha’awarsa da yawaita yin azumi, da zama da yunwa, da karanta cin abinci[15].

3- kokarin ganin ya yi maganin duk wata hanya da takan iya kai shi ga jin sha’awa, kamar; tunanin abubuwan da sukan jawo masa sha’awa, da magana da mata, da kallon mata, da kebewa da mace, da kallon fila-filan banza da dukkan wani abu da zai iya sanya shi jin sha’awa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next