Zabar Mace Ko Namijin Aure



Mace mai son duniya ba abin da ta sani sai wahalar da miji da gasa da sauran mata wajan tara abin duniya, wani abin haushi shi ne kakan ga mace duk wani yadi da ake yayi, ko wata kwalla, ko tangara, da sauran kayan karau, sun san shi da kyau, amma ba zaka taba jin sun san wani abu littafi kaza kan ilimi kaza da aka buga kwanannan ya fito ba, kai abin ma har ga maza, ba zaka taba jin sun san kaset kaza sabo a kan ilimi kaza ya fito ba, wannan kuwa yana daga cikin mummunar tarbiyyar da aka samu na zaman banza da kashe wando da hirar duniya da ba abin da aka sani sai dai gulma da gasar tara kayan duniya da juna da mata suka samu kansu a ciki.

Sannan wannan ya taso daga mummunar al’adar nan ta rashin wayewar yin rubutu da ba wa ilimi muhimmanci da hatta da littattafan Hausa sai dai ka ga an rubuta su a wasu kasashe daga wasu mutane wadanda ma ba Hausawa ba ne, amma su Farfesa wane, da Dakta wane, da Alhaji wane, ba abin da ya rage musu sai sunan kawai, kuma ba su da wayewar karfafa wa al’umma ilmantuwa da yarenta ta hanyar ilimi da kuma kudi da Allah ya ba su, ta yadda da zaka dauki yaren Hausa zaka ga babu wani abin a zo a gani na ilmi da aka rubuta da shi, ko fassara Ilimin wasu nahiyoyi da shi.

Amma zaka ga duk wani kaset na waka da wanda yake haramun ma a jinsa, kamar mai halatta haram ko wanda yake cike da kalmomin sabo iri-iri, sun san shi, da wani kaset na sabuwar waka ko sabon wasa ya fito yanzu ka ga suna nemansa.

Wannan ba ya rasa nasaba da irin miyagun al’adun da aka taso a kansu na rashin kokarin ganin an kashe jahilci, Shi ya sa zaka ga mace tana da duk wani abin rayuwa a dakinta, ko kuma tana hankoron samunsa, amma da za a ce a fito da littafi daya na ilimi daga cikin dakin ko wane iri ne, da ba a samu ba, tayiwu ka sami na tatsuniya da ba shi da amfanin komai a rayuwa, maimakon ta yi murna da cewa kwabarta ta cika da littattafan ilimi, sai tana alfahari ne ga sauran kawaye da kwaba ta cika da kayan alatu. Amma a gane ba muna cewa laifi ba ne tara kayan duniya, sai dai muna cewa ne kada su zama hadafi na farko a rayuwa kamar yadda muke bayanin hakan, kuma kada a manta da ilimi da wayewar rubuce-rubuce.

Har ma kakan samu mata wadanda zuciyarsu ta yi tsatsa da son abin duniya Suna yin kawa da wasunsu ne saboda abin duniya ya cika dakinsu, kakan ga mata suna maganar wance abin nata gwanin sha’awa, amma da zaka tambayi dalili da sai ka ga ashe dakin ya cika ne da abin duniya.

Haka nan wata rana a wani ajin karatu a Jami’a a Farisa malama Mitra ta yi dariya ga irin wannan dabi’a da al’ada ta kasala, da lalaci, da rashin ko in kula da batun Ilimin mace a al’ummarmu, take cewa: “Ta je wani gida na Hausawa da ke nan Tehran sai ta ce da matar gidan ta kunna mata kwampita zata yi taipin (rubutu), sai matar ta ce ba ta iya kunnawa ba, alhali kwampitar ta yi shekaru a dakinta, Sai dai mijin ya kunna ya yi aikinsa ya kashe, amma wannan bai taba sanyawa ta yi koda tunanin ya koyar da ita komai ba”. Haka sakamakon rashin kumaji da zil da rashin motsi, da rashin sa ran ci gaba a al’umma, da miyagun al’adu, sukan sanya mata har ma da maza su zauna a dankwafe ba ci gaba.

Dole ne malamai su shagaltu da wa’azi don shiryar da al’umma ta kafofi daban-daban, kuma a shagaltu da yin kaset-kaset na ilimomi daban-daban, a kuma bude wajajan sayar da su ta yadda idan mace ko namiji yana son jin Ilimin Tafsiri, ko Akida, ko Fikihu, ko Tarihi, ko Nahawu, ko Hadisai, ko Zamantakewar al’umma, ko Tattalin arziki, da sauransu ya zama akwai kaset cikakke kan wannan ilimi da zai iya sanyawa ya ji, wasu kuma su shiga wallafa ko fassara littattafai da yada su kan wadannan ilimomi, sa’annan su shagaltu da wayar da kan al’umma kan kokarin karatu da rubutu, wannan kuwa ya zamanto duk da harshen Hausa da al’ummarmu take fahimta, Sai ya zama mutane da yawa sun san ilimi daban-daban ta hanyar yarensu.

Game Da Soyayya

Saboda haka duk wanda zai yi aure to lallai ya lura da siffofi na gari tukuna kafin wani abu ya biyo baya, Sannan ya zama a bisa soyayya da kaunar juna. Wani abokina ya ba ni labari cewa, wata rana yana cikin add’ua Allah ya ba shi mata ta gari, Sai wani tsoho ya ce: Ka ce Allah ya ba ka mata mai sonka yaro, Idan ka samu, ka samu ta gari, ya ce: Bai san muhimmancin maganar ba sai da ya yi aure.

Kamar yadda Shehu dan Fodio (R.A) ya kawo kashe -kashen nau’o’in so[36], So kala-kala ne, wasu daga cikinsu shi ne: So na imani, irin wannan son shi ne wanda ake wa Allah da Manzonsa da Imamai da waliyyai da sauransu, misali a cikin littafin Nahajul balaga Sayyidi Ali (A.S) yana cewa: Da na sari hancin mumini da takobina wannan a kan ya ki ni da bai ki ni ba, kamar yadda da na tara wa munafuki duk duniya gaba dayanta a kan ya so ni da bai so ni ba, saboda an riga an hukunta ya kuma zartu a harshen Annabi Ummiyyi (S.A.W) cewa: Ya Ali! Munini ba zai taba kin ka ba, kuma munafuki ba zai taba son ka ba[37].

Haka nan Imam Ali (A.S) ya taba yanke hannun wani barawo bayan barawon ya fita daga wajansa, sai wasu muminai suka hadu da shi a hanya, suka ji yana ta yabon Amirul mimin (A.S) Sai suka zo suka gaya wa Imam Ali (A.S) suna mamakin irin yabo da godiya da yake yi wa Imam din, Sai Imam ya yi umarni a ka kirawo shi ya mayar masa da hannun.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next