Zabar Mace Ko Namijin Aure



15- Rashin halaccin cin sadakin mace ga miji yayin rabuwa: Bakara: 229.

16- Sulhu tsakanin miji da mata: Nisa’I: 35[17].

Nutsuwar Ruhi Tana Samuwa Ta Hanyar Aure Ne

Samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama ba ya yiwuwa sai ta hanyar auratayya, domin idan ta fuskar fasikanci ne ake zaune da juna wannan nutsuwar ruhi har abada ba ta samuwa, wannan kuwa abu ne sananne da dabi’ar halittar mutum, da ilimi, suka gaskata da shi.

Saboda haka duk wanda zai yi aure ya tuna ko ta tuna cewa za ta yi aure ne da wanda zasu zauna domin gina rayuwa maras iyaka da gina gida salihi. Amma tambaya a nan ita ce: Wane mutum ne zamu zaba domin wannan rayuwa da kuma samun nutsuwa, da soyayya, da tausasawa, da tausayawa juna?.

Alaka Da Juna Kafin Aure

Ba a son a samu shakuwa sosai sai da wanda za mu yi aure da shi, saboda haka irin soyayyar da ake yi ta al’adun da suka shigo cikin al’ummar Hausa musamman daga yammacin duniya ba ta da kyau matukar ba aure za a yi ba, domin saudayawa takan kai ga aikata haram wanda zai yi tasiri a kan saurayi da budurwa har karshen rayuwarsu, kuma saudayawa rayuwar ‘yan mata ta lalace ta hakan sakamakon irin wadannan miyagun al’adu.

Saudayawa mace mai saukin hali da samari sukan iya shawo kanta ta hanyoyi daban-daban wani lokaci ma har wani shakiyyi yakan ce da ita: Idan kika yarda da ni muka kwanta to lallai zan aure ki. Irin wannan da yake son sha’awa ne ba na Allah da Annabi ba, da zaran ya san ta a ‘ya mace sai ya yi wurgi da ita, ya watsar, ba ma zata san cewa mugu ba ne mai tsananin wulakanci sai idan ta samu cikin dan shege ta wannan mummunar hanya, a lokacin ne zata san cewa ba ya kaunarta koda kwayar zarra. Saudayawa a kasashen duniya da kasashenmu ‘yan mata suka kashe kan su saboda wannan mummunan hali da mayaudaran samari suka jefa su a ciki, rayuwa ta gurbace musu[18] suka koma abin tausayi bayan da suna abin haushi, ko kuma suka gudu daga garuruwansu, ko ma suka haife dan amma suka yarda shi a kwararo suka gudu.

Da yawa mata suna da saukin hali shi ya sa suka yaudaru da wuri, wasu kuma kwadayi ne yakan kai su ga fadawa irin wannan mummunan hali, don haka yana kan iyaye su rika sanin menene ‘yarsu take yi a waje, kuma da wadanne irin kwaye ne take mu’amala, sannan kuma su waye suke zuwa zance wajenta da sunan suna son aurenta.

Dalilin Wali Ga Budurwa

Mace da yake tana amfani da dabi’ar zuciya ne[19] wajan so ko kin abu, shi ya sa musulunci bai ba wa budurwa ikon yin aure ba sai da hannun waliyyanta in suna raye, domin mace musamman budurwa saudayawa idan abu ya kayatar da ita ba tare da ta kalli karshensa ba tana iya gaggautawa zuwa gareshi, wannan yana daga cikin aiki da dabi’ar zuciya. An sanya wa budurwa wajabcin yardar waliyyinta ba don namiji ya fi ta hankali ba, sai don mafi yawan maza sun fi yin amafani da shi in an kwatanta da mafi yawan mata, wani yakan iya cewa: Ai a kwai Hadisi da ya nuna namiji ya fi mace hankali. Sai na ce: Hadisin ya fassara abin da yake nufi da karancin hankali, wato saudayawa sukan fi namiji mantuwa yayin da mai tsira da aminci yake cewa da wasu mata: Ashe (ba a sanya) shedar mace kamar rabin shedar namiji ba? Suka ce: haka ne. Sai ya ce: Ai wannan shi ne daga tawayar hankalinta. Ashe idan ta yi haila ba ta salla, ba ta azzumi ba? Suka ce: haka ne. Sai ya ce: Ai wannan shi ne daga tawayar addininta[20].

Sannan kuma akwai Hankali na dabi’ar mutum da al’umma take gani da tunani ta hanyarsa, da su matan a kan kansu aka sanya musu cewa haka suke, wato tunanin al’umma haka yake ganin su har wannan ya zama jiki gun maza da mata, domin su ma wani bangare ne na al’ummar, kamar yadda irin wannan tunanin da yake tafiyar da al’amarin al’umma, wanda ya sanya mata suke ganin maza suna da matsala, su ma maza suna ganin mata a hakan.

Amma sanannen abu shi ne Allah ya halicci maza da mata da dabi’a iri daya ta hankali, sai dai a kan sami wani ya fi wani amfani da shi da kuma hangen nesa, namiji da mace a nan babu bambanci. Duba ka ga Bilkisu[21] da Mutanenta da kaifin basirarta duba sayyida Maryam da sayyida Hadiza da sayyida Fadima (A.S) a cikin al’ummarsu, sai dai Annabi (S.A.W) yana magana da mutane daidai hankulansu da fahimtarsu ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next