Zabar Mace Ko Namijin Aure



e- Idan ma’abota wannan halin ba a shirye suke su yi aure ba koda kuwa suna da yalwa, to musulunci har yanzu ya ba su damar yin auren mutu’a, don haka ne ma idan irin wadannan wajajen ba zasu kullu ba, sai wadannan mata masu zaman kansu su tuba daga wannan ayyuka, maimakon su rika zina sai su yi auren mutu’a da duk wanda suke so, bayan muddar ta kare sai su yi idda. Wasu malamai suna ganin gwamnatin musulunci tana iya mayar da gidajen banza su koma gidajen shari’a ta wannan hanya, musamman gudun cewa irin wadannan mutane idan aka kore su, to zasu koma suna fasikanci a boye, maimakon haka sai su tuba su bi hanyar da shari’a ta gindaya musu.

3- Rashin yalwa da talauci da tsadar aure: yana daga cikin abin da kan kawo jinkirin aure ga samari, don haka bai kamata ba a bi al’ada da kuntatawa da tsanantawa ga kudin aure da zata kai ga wannan jinkiri har ruhin samari da budurwa su gurbata da ciwowwuka, ko miyagun halaye, saudayawa jinkirin yana faruwa sakamakon:

a- Sanya sharudda masu wahala ga saurayi.

b- Yawan kudin da zai kashe kan kayan tanadin gida da sauransu.

A game da matsalar farko, al’umma ne ya kamata su sanya hannu wajen warwareta, amma matsala ta biyu al’umma da hukuma su ne zai zama sun sanya hannu wajen maganinta.

4- karancin amintuwa da juna tsakanin saurayi da budurwa, musamman akan samu wasu da yawan munana zato ga duk wanda suka hadu da shi, ta yadda yakan yi musu wahala su yarda da shi[5].

Ta wani bangaren kuma wani lokaci jinkirin yakan taso ne saboda ruwan ido ko kuma tsanantawa wajen sharuddan saurayi ko budurwa da zasu aura wanda wannan ya kan daukar musu tsawon lokaci ba su samu mai wannan sharuddan ba, ko ma suka samun mai wadannan sharuddan. Mu sani binciken halin wanda za a aura saurayi ne ko budurwa yana da kyau, amma kada ya kai ga matsananci da zai fita daga al’adarsa.

Warware wannan matsalar yana hannun samari da ‘yan mata ne.

Wasu Matsalolin Da Akan Iya Fuskanta

Wasu daga Matsalolin da saurayi ko budurwa kan iya fuskanta kafin aure ko bayan aure: Wani lokaci saurayi da budurwa sukan fuskanci matsala ne kamar haka:

1- Burin da kowane bangare da iyayen saurayi da budurwa, ko su kansu saurayi da budurwa suke ci game da saurayi ko budurwa. Kamar kayan daki da yake tunanin a kawo ta da shi da sauransu, ko kuma shi kayana da take tunanin ya kai gidansu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next