Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



 Muna iya amfana daga ayoyin Kur’ani da suke nuni da cewa: Al’ummun da suka gabata sun kasance suna kiyaye duk wani abin da manzonsu ya zo da shi, ta yadda suke tafiya da shi yayin wani kwami mai zafi da yake a gabansu. Ta yadda ta hanyar neman albarkaci da wannan abin daga annabawansu don neman samu cin nasara daga mushrikai abokan gabarsu.

 A matsayin misali Bani Isra’il sun kasance suna tsaron wani akwati wanda duk abin da musa da iyalansa suka bari yana cikinsa, sannan suna neman tabarruki daga gare shi kuma yayin karo da makiya suna daukar shi domin neman cin nasara.[9]

 Kasantuwar albarkar da muhimmancin wannan akwati ya zamana mala’iku suke daukarsa. Idan har ya kasance kiyaye wasu abubuwa na magabata (kamar wannan akwatin) wani abu ne marar kyau, to me ya sa Kur’ani mai girma yake ambaton wannan al’amari da harshe na yabo, kuma me ya sa mala’iku suke daukarsa, sannan me ya sa bayan dauke wannan akwati daga "Amalika" a cikin wannan aya ya zama wata alama ce da take nuna wanda zai jagoranci wannan runduna ta yaki?!

 Yara wadanda ba su balaga ba, su ne suke wasa da kayan da iyayensu suka bar musu, ta yadda cikin sauki suna iya batar da su. Amma magadan da suke da hankali kuma sukan amfani da matsayin wannan abin da iyayensu suka bar musu, suna rike wadannnan kaya ne iya karfinsu. Al’ummar musulmi ma sakamakon cigaban da suka samu bayan wafatin Manzo (S.A.W), su kiyaye duk wani abu da ya bari, wannan kuwa har da kwarar gashinsa sun kasance sun sanya ta wani wuri na musamman suka ajiye ta.

 

Matsayin Gidajen Annabawa A Cikin Kur’ani

 Gidajen annabawa da manyan bayin Allah suna da wani matsayi na musamman, wannan kuwa a fili yake matsayin da suke da shi bai shafi wani abu na duniya ba ne, domin idan da haka ne, gidajensu ba su da wani bambanci da sauran gidajen mutane domin an gina su ne da yumbu da tubali kamar na kowa. Wadannan gidaje suna da wannan matsayi ne sakamakon mutane masu matsayi da suka zauna a cikinsu.

 Kur’ani mai girma[10] yana siffanta hasken ubangiji da fitila mai haske ta yadda yake haske kamar tauraruwa. A ayar da take biye ma wannan aya kuwa ya nuna cewa wurin wannan haske yana gidajen wasu mutane masu girma wadanda suke ambaton Allah a ciki safiya da yamma.[11]

 A cikin wannan aya jimlar da take cewa "Ana tasbihinsa safiya da yamma, tana nuna dalilin da ya sa aka daukaka wadannan gidajen wadanda aka ambata a cikin ayar da ta gabata. A ayar da take biye mata kuwa an siffanta masu yin ibada a cikin wadannan gidaje ne, inda yake cewa: "mutane ne wadanda kasuwanci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsayar da salla, domin suna jin tsoron ranar da zukata da idanu suke jujjuyawa suna tsorata.[12]

 Wannan aya tana bayani ne a kan girma da daukakar gidajen da ake zikirin Allah ake kuma tsarkake shi a cikinsu. A nan dole ne mu yi bayani a kan abubuwa guda biyu kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next