Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



 Wanda kafin ya fara bayyana kiransa ya kasance yana tafiya kogon hira domin yin ibada ga Allah madaukaki. Bayan cika shekara arba’in da rayuwarsa ya fara kiransa. Wasu mtane daga cikin mutanen Makka suka yi imani da shi, yayin da wasu mafi yawa suka kaurace masa, har ma suka yi nufin su hallaka shi, amma Allah da ikonsa ya boye shi a wani kogo da ake kira (Thaur) wanda yake kudancin garin Makka, ta yadda ya tsira da makiya. Bayan nan kuma ya yi hijira zuwa garin Madina, a wannan gari ne mutane Aus da Khazraj (wadanda ake kira da Ansar) suka amsa kiransa suka taimake shi. Manzo a tsawon zamansa a garin Madina ya gwabza yaki mai tsanani tsakaninsa da mushrikai da Yahudawa, Ta wannan hanyar ne ya gabatar da shahidai da dama a tafarkin Allah ta yadda suka ba da jinansu a yakin Uhud, Khaibar da Hunain. Manzo (S.A.W). Ta hanyar aika mabiyansa zuwa sassa daban-daban na wannan nahiya ta kasashen larabawa ya samu damar isar da sakonsa zuwa ko’ina a wannan lokaci. A shekara ta 11 ne bayan hijira ya koma zuwa ga ubangijinsa kuma ya yi umarni da rufe shi a cikin dakinsa. Bayan wafatinsa mabiyansa suka cigaba da hanyar da ya bari, ta yadda ba tare da bata lokaci ba, ya yada wannan addini tare da al’adun da Kur’ani ya zo da su a dukkan sassan duniya.

 Wannan shi ne wani yanki na tarihimmu wanda bayan wucewar karni 14 ake maimaita shi. Saboda haka dole mu yi kokarin wajen kare wannan tarihi na mu da duk abin da ya shafi hakan, ba wai ta hanyar wasu dalilai ba marasa tushe mu ruguza wannan tarihi namu!.

 Kamar yadda ya kasance mu shagala game da kiyaye wadannan kayan tarihi, ta yadda babu bambanci a wurin dangane da samuwarsa da rashinsa duk daya yake, (abin da ma ya fi muni shi ne yadda ake ganin cewa rusa wadannan abubuwa yaki ne da yaduwar shirka) Ta yadda a cikin kankanin lokaci an manta da wasu abubuwa na tarihin musulunci, don ha ka bayan wani lokaci zai yiwu a fara shakku dangane da wasu abubuwa na hakikanin wannan kira da Manzo ya zo da shi. Ta yadda kamar su Salman Rushudi maimakon canza addini sai ya yi kokarin inkarin addinin da tarihinsa baki daya.

 

Daukar Darasi Daga Tarihi

 Mutum kodayaushe yana kokari ne ya kalli kowane al’amari ta hanyar idanu ko makamancinsu, domin kuwa ilimin da yake samuwa ta wannan hanya mutum ya fi dogara a kansa. Cikinsa a babban hanyar da ake bi domin tabbatar da wani abu dangane da abin da ya shafi rayuwar zamantakewa, kuma wanda aka fi dogara da shi domin yana ba da sakamakon da ake samun yakini, shi ne tarihi, Kur’ani mai girma yana ba da tarihin magabata ne domin daukar darasi. [8]

 Dangane da shari’un da suka zo daga sama muna iya daukar shari’ar Annabi Isa (A.S) a matsayin misali. A akidar musulmi Annabi Isa matsayin annabin Allah yake, wanda yake mai albishiri ne ga zuwan Manzo Muhammad (S.A.W), sannan ya zo da littafi mai suna "Injil" wanda yake dauke da haske a cikinsa, amma muna samun tabbas a hakan ne ta hanyar Kur’ani mai girma.

 Amma sakamakon matashin da yake yammacin duniya ba shi da imani da Kur’ani ta yadda zai kalli Annabi Isa ta wannan fuskar, a yau dangane da zuwan Annabi Isa da littafinsa yana da shakku a kansu. Domin kuwa ba shi da wata alama ta wannan kira a hannunsa ta yadda zata taimaka masa ya samu yakini a kan hakan. Domin kuwa Masih ba shi da kabari ko mahaifiyarsa da sahabbansa da zasu tabbatar da zuwansa. Sannan littafinsa an hakaito shi ta hanyoyi daban-daban ta yadda zai yi wahala mutum ya gane gaskiyar al’amarin.

 A takaice babu wani abu wanda zai tabbatar wa matashin yammacin duniya gaskiyar zuwan Annabi Isa da littafinsa. Saboda haka sabanin magabatansa yana shakku a kan hakikanin wannan al’amari.

 Saboda haka mu musulmi dole mu dauki darasi daga wannan abin da yake faruwa daga kiristanci. Ta yadda zamu kiyaye duk wani abu wanda yake ya zo daga Manzo kuma yana matsayin sheda ne ga da’awar da shi Manzo ya zo da ita, (duk yadda ya kasance abu dan karami ne) Ta yadda zamu kare duk wani abu wanda zai sanya wadanda zasu zo bayammu su yi shakku a kan gaskiyar addinin musulunci, kamar yadda matashin yammacin duniya yake shakkun gaskiyar Annabi Isa da Injila.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next