Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



D-Girmama Kabarinsa da yin gini domin kiyaye shi daga lalacewa;

Aikata wadannan abubuwa da makamantansu wadanda suke sun halasta a musulunci, yin su ga Manzo da iyalan gidansa ya nuna kauna ne a gare su.

Tirmizi yana ruwaitowa a cikin sunan dinsa: "Manzo (S.A.W) ya kama hannun Hasan da Husain sai ya ce: Duk wanda yake so na ya kuma so wadannan yara guda biyu da babansu da mamansu, to zai kasance a matsayina a ranar kiyama[26].

 Kowannenmu ya san da cewa babban jikan Manzo yana rufe ne a"bakiyya" Sannan mai biye masa yana rufe a Karbala, Sannan wadannan wurare kodayaushe suna ganin al’ummar musulmi masu ziyara, Saboda haka duk wani gini kowane abu wanda za a yi domin kiyaye wadannan wurare, nau’i ne na nuna soyayya ga wadannan jikoki na Manzo kuma bin umarnin Manzo ne a kan soyayya gare su, kamar yadda muka yi bayani a ruwayar da ta gabata.

 A yau al’ummu da dama suna kokari wajen tunawa da manyan tarihinsu (kamar sojoji da ‘yan siyasa da wadanda suka yi wasu ayyuka na gyara) ta hanyoyi daban-daban, sakamakon haka ne suke halarta jana’izarsu yadda ya kamata. Sannan su rufe a wani wuri na musamman a karkashin gini mai kawatarwa, ta yadda wadanda zasu zo a nan gaba kamar yadda na yanzu suke kulawa ta musamman a kan su, suma su yi kulawa da girmamamawa ta musamman a kan wadannan manyan mutane. Don haka mu ma musulmi dole mu yi kokari don yin gine-gine da zasu kare kabuburan manyan mutanemmu.

 

Kaburburan Manzanni Da Tarihin Magabata Ma’abota Taihidi

 Tafiye-tafiye domin bude ido zuwa wuraren da aka rufe annabawa da ‘ya’yansu wani abu ne wanda yake ba sabo ba a cikin al’umma. Wannan kuwa yana nuna cewa mabiya annabawa suna nuna kulawa ta musamman dangane da wadannan wurare, tare da gina gine-gine a kan kaburburansu suna kare su daga rushewa. A yanzu a kasashen Iraki, Palasdin, Jordan, Misra da Iran, akwai kaburburan annabawa (A.S) wadannan aka yi gine-gine masu kawatarwa ta yadda kodayaushe mutane suna zuwa wurin domin ziyara. Sannan dakarun musulunci da su kai hare-hare don bude garuruwan Sham, sam ba ruwansu da wadannan kabuburan annabawa, ba ma haka ba kawai sun bar mutanen da suke hidima a wadannan wurare don su cigaba da aikinsu a wajen kamar yadda suke a da. Sannan ba su nuna rashin amincewarsu a kan hakan ba ko kankani. Idan da yin gine-gine a kan kaburburan annabawa wani aiki ne da ya haramta kuma ya shafi shirka, da wadannan dakaru da suka zo da umarnin khalifa domin bude wadannan garuruwa duka sun rusa wadannan gine-gine, amma koda wani dan karamin canji ba su yi ba ga wadannan kaburbura an cigaba da tafiyar da su kamar yadda suke kafin wannan lokaci. Sannan har zuwa yanzu wadannan gine-gine suna nan kamar yadda suke ta suke jawo hankalin al’ummar musulmi da ma duk mai bin addinan da Allah ya aiko da su.

 Sannan a farkon zuwan musulunci ma musulmai sun rufe annabinsu a cikin dakinsa, kuma babu wani daga cikin wadannan musulmai da yake tunani cewa yin gini a kan kabarin Manzo haramun ne.

 Sannan binciken littattafan tarihi da labaran tafiye-tafiyen masana addinin muslunci yana bayar da shedar cewa akwai daruruwan kaburbura a kasar da wahayi ya sauka da sauran kasashen musulmi:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next